✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattijo ya shiga hannu kan zargin yin luwaɗi da yaro a Zariya

Rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike za ta miƙa wanda ake zargin zuwa kotu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wani dattijo mai shekara 55 a duniya, da ake zargi da yin luwaɗin da wani yaro ɗan makarantar firamare a Zariya.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, ASP Mansur Hassan ne, ya tabbatar wa Aminiya kamen.

Ya ce ana zargin dattijon ya ɓata wani ƙaramin yaro ɗan shekara takwas a duniya.

Ya ce makusantan yaron tare da gudunmuwar al’ummar Anguwar Tudun Jukun da ke Zariya ne, suka miƙa wanda ake zargin ofishin rundundar da ke Tudun Wada Zariya.

Rundunar ta bayar da umarnin kai yaron asibiti domin yi masa gwaji kafin tabbatar da laifin wanda ake zargin.

Kakakin ya ce wanda ake zargin, yana hannun inda ake gudanar da bincike a kansa.

Ya ce zarar sun kammala bincike za su gurfanar da dattijon a gaban kotu.

Aminiya ta ziyarci cibiyar kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba, domin samun bayani game da lamarin.

Manajar cibiyar, Hajiya A’isha Ahmed, ta ce a ranar 21 ga watan Oktoba 2024, aka kai musu ƙarar wani da ake zargi da ɓata ƙaramin yaro.

A cewarta likitoci sun duba yaron tare da tabbatar da cewar an yi luwaɗi da shi ta dubura.

Ta ce tuni aka ɗora yaron a kan magani har na tsawon kwanaki 28 kuma za su riƙa bibiyarsa domin tabbatar da cewa yana amfani da maganin yadda ya kamata.

Kazalika, ta ce da zarar sun kammala haɗa rahotonsu, za su miƙa shi ga rundunar ’yan sandan jihar domin ɗaukar mataki na gaba.

Sai dai ta yi kira ga iyayen yara da su daina ɓoye irin wannan lamarin, domin hakan na iya shafar rayuwar yaran a gaba.

Ta ƙara da cewa zuwa asibitin da yaran da aka ci zarafinsu a kan lokaci yana taimakawa wajen kula da lafiyarsu.