✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe ’yan sanda 4 a Katsina

Maharan sun hallaka ’yan sanda huɗu tare da raunta wasu.

’Yan bindiga sun kai hari wani sansanin ’yan sanda a Jihar Katsina, inda suka kashe jami’ai huɗu da wasu mutum biyu.

Sun kai harin ne sanssnin ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke Garagi, a Karamar Hukumar Kankara.

Mazauna garin sun ce maharan sun kashe jami’an tsaro huɗu tare da raunta mutum ɗaya.

Har wa yau, maharan sun yi awon gaba da bindigogin ’yan sanda.

Kazalika, sun kashe wasu mazauna garin guda biyu.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun ƙone azuzuwan makarantar firamaren Tsamiyar Jino, inda jami’an tsaron suka kafa sansaninsu.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.