Wasu ‘yan bindiga sun harbe ‘yan sanda biyu da wani matashi har lahira a mahadar Ahiara da ke Karamar Hukumar Ahiazu Mbaise ta Jihar Imo.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, maharan sun bude wa jami’an tsaron wuta ne yayin da suke bakin aiki.
- Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane biyu a Taraba
- Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, ya kuma shaida wa NAN cewa wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wane ne ba ya mutu sakamakon wani harsashi da same shi a lokacin harin.
“Suna zuwa suka bude wuta kan ‘yan sandan inda suka kashe biyu nan take.
“Harsashi ya kuma samu wani matashi kuma nan take shi ma ya mutu.
“Wannan abin takaici ne sosai,” in ji majiyar.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda rundunar, ASP Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Okoye ya ce rundunar ta fara farautar ‘yan bindigar da suka aikata wannan ta’asar.
Ana iya tuna cewa a ranar 19 ga watan Satumba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a yankin Umualumaku na Karamar Hukumar Mbano a jihar.
‘Yan bindigar sun kashe tare da kone jami’an tsaro akalla biyar a lokacin harin.