✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida

Furodusan ya ce marigayin ya taimaka sosai a harkar sana'arsa.

Darakta kuma furodusa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Abdul Amart Mai Kwashewa, ya saya wa iyalan marigayi Aminu S. Bono gidan zama.

Aminiya ta ruwaito cewa mutuwar Darekta Bono ta girgiza masana’antar Kannywood wanda a ranar 20 ga watan Nuwamba nan Allah Ya karɓi rayuwarsa Kano.

Amart wanda shi ne shugaban kamfanin Abnur Entertainment, ya ce suna tunanin yadda za su taimaka wa iyalan Bono ne sai ya samu labarin cewa kudin hayarsa zai kare a wannan wata.

“Mutum ne (Bono) da ya kamata tsakani da Allah mu tsaya masa, mu tabbatar ‘ya’yansa sun taso cikin aminci, shi ne karshen kauna da za mu iya nuna masa.

“A shawarce, sai na ce a nemo gida a kusa da gidan iyayensa, Allah kuma cikin ikonsa, ban shirya ba, Allah Ya taimake ni na yi wannan abun,” in ji Mai Kwashewa.

“Mutum ne da ya taimake ni a harkar sana’ata, da me zan saka masa, shi ne na rike masa iyalansa. In Allah Ya yarda ba za su wulakanta ba saboda kyawawan halayensa.”

Mai Kwashewa na daya daga cikin na hannun daman marigayi Bono, wanda ya yi aiki karkashin kamfanin Abdul Amart tun kafin ya yi suna.