✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane biyu a Taraba

Sojojin sun bukaci hadin kan jama'ar jihar don inganta aikinsu.

Dakarun sojoji a Jihar Taraba, sun kama wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.

An ruwaito cewa sojojin sun kama wadanda ake zargin tare da ceto mutanen a yankin CBN/Baba-Yau a Jalingo a ranar Lahadi.

Bayanai sun ce daya daga cikin wadanda aka ceton ya koma ga iyalansa yayin da dayar ke karbar magani kafin komawa ga iyalanta.

Kwamandan birgediya ta 6, Birgediya Janar Frank Etim, wanda ya yabawa dakarun, ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai da goyon baya.

Ya jadadda muhimmancin samar da bayanan tsaro domin inganta aikinsu da kuma kai dauki a kan lokaci.