Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki a unguwar Gbagy Villa da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, suka kashe mutum daya sannan suka sace wasu 10.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani a kan harin da ’yan bindigar suka kai a cikin daren ranar Litinin.
- AFCON: Shin Najeriya za ta iya lashe Gasar Kofin Afirka?
- Bayan shekara 10, an dage haramcin amfani da babura a Yobe
Wani mazaunin unguwar da ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsaro ya ce, “Sun shiga gida-gida suka dauki mutane sannan suka kashe wani mutum daya.”
Aminiya ta gano cewa daga cikin wadanda maharan suka sace a yayin harin, akwai mata da kananan yara.
Wani jami’in rundunar tsaron sa-kai (JTF) a yankin ya tabbatar da mutuwar mutum daya a sakamakon harin.
Kwao yanzu dai babu wata sanarwa game da harin daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, kakakinta kuma, ASP Jalige Mohammed, bai samu daukar kiran wayar wakilinmu ba, ballantana mu ji ta bakinsa.
A makonnin da suka gabata ne mazauna unguwannin Juni, Unguwar Gimbiya, Kauyen Oil, Sabon Tasha GRA da Unguwar Barde, duk a Karamar Hukumar Chikun suka fuskanci munanan hare-hare daga ’yan bindiga.