✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mafarauta 18 a Taraba

’Yan bindigar sun yi galaba ne a kan mafarauntan sanadiyyar miyagun makamai na zamani da suke dauke da su.

’Yan bindiga sun kashe mafarauta 18 a wasu hare-hare mabanbanta da suka kai a Karamar Hukumar Bali da ke Jihar Taraba.

Aminiya ta ruwaito cewa an kashe mafarauta 15 a wata arangama da ’yan bindiga a wani tsauni da ke kusa da garin Maihula a ranar Talata.

Bayanai sun ce ’yan bindigar da yawansu ya haura 200 sun yi yunkurin kai hari a garin Bali, hedikwatar Karamar Hukumar Bali da wasu kauyukan da ke kewaye amma mafarautan suka tunkare su.

An kuma ruwaito cewa, ’yan bindigar sun yi galaba ne a kan mafarauntan a sanadiyyar miyagun makamai na zamani da suke dauke da su.

Wani da mazaunin yankin da Aminiya ta zanta da shi mai suna, Musa Umar, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mafarauta 14 a yayin arangamar, yayin da cikon na 15 din da samu raunuka ya riga mu gidan gaskiya a kan hanyar kai shi Asibitin Jalingo.

.Shugaban kungiyar mafarauta na Jihar Taraba, Adamu Dantala ya tabbatar wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kashe mambobinsa 15 a yayin arangamar.

Kazalika, ya ce ’yan bindigar sun yi wasu mambobinsa kwanton bauna a kauyen Dakka da ke Karamar Hukumar ta Bali, inda a nan ma suka kashe wasu mafarautan uku.

Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki musamman ta fuskar makamai masu inganci tun da a cewarsa babu wani tallafi da ake ba su domin kula da iyalan wadanda suka rasu ko kuma suka jikkata.

Sai dai kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi da Aminiya ta tuntuba domin neman karin haske a kan lamari, an yi rashi sa’a bai amsa kiran wayarsa ba ballanta kuma ya bayar da amsar sakon kar ta kwana da aka aike masa.