✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai harin daukar fansa ofishin ‘yan sanda a Zamfara

’Yan ta'adda sun kashe dan sanda da tsararru shida a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Zurmi a Jihar Zamfara

’Yan bindiga sun kashe dan sanda a harin da ’yan ta’addan suka kai a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Zurmia Jihar Zamfara.

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa baya ga dan sandan da ya kwanta dama, maharan sun kashe wasu mutum shida da ake tsare da su a ofishin ’yan sandan.

Mazauna garin Zurmi sun ce a yammacin ranar Lahadi ne dandazon maharan suka kutsa cikin garin inda kai-tsaye suka wuce zuwa ofishin ’yan sanda, suka bude wa jami’an da ke bakin aiki wuta.

Ana zargin harin na daukar fansa ne saboda ’yan banga sun kashe wasu ’yan bindiga biyu a garin.

Kakakin ’yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da harin, inda ya kara da cewa an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin, kuma kura ta lafa.

Rundunar ’yan sandan jihar ta kuma lashi takobin kamo wadanda suka yi wannan ta’addancin a garin Zurmi.

Karamar Hukumar Zurmi na daga cikin yankunan Jihar Zamfara da ke sansanonin ’yan bindiga.