✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe kasurgumin dan bindiga Mai Dubu-Dubu a Sakkwato

Kasurgumin dan bindiga Bello Hantsi (Mai Dubu-Dubu) ya sheka lahira bayan ’yan sanda sun bindige shi a Jihar Sakkwato.

’Yan sanda sun aika kasurgumin dan bindiga Bello Hantsi, wanda aka fi sani da Mai Dubu-Dubu, lahira a Jihar Sakkwato.

Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, ya ce jami’an rundunar sun kwato makamai daga Mai Dubu-Dubu bayan da suka aika shi barzahu a Karamar Hukumar Kware.

Sanarwar da ya fitar ta ambato kwamishinan rundunar, Ali Hayatu Kaigama, yana cewa Mai Dubu-Dubu da aka kashe a kauyen Tungar Rana yana daga cikin dillalan makamai da ke sayar wa sauran ’yan bindiga.

“Da misalin karfe 0330 na dare Babban DPO na yankin Kware da jami’ansa suka je farautar Mai Dubu-Dubu a wani daji bayan sun ga alamar motsinsa.

“Ko da dan bindigar ya gan su, sai ya fara harbi yana kokarin tserewa, amma ba tare da bata lokaci ba jami’anmu suka harbe shi har lahira, sauran abokansa kuma suka tsere da raunin harbi a jikinsu.

“Mun dauko gawarsa kuma a wajen da muka kashe shi mun samu bindiga kirar AK-47 guda daya da harsasai 21,” in ji sanarwar.