Barawon da ya caka wa wata budurwa wuka ya kwace wayarta a garin Damaturu na Jihar Yobe ya fada komar ’yan sanda.
A kwanakin baya ne dai wani barawon waya ya kwace wayar budurwar bayan da ya caka mata wuka a gidan baya a unguwar Malari a garin Damaturu fadar.
Sakamakon haka aka garzaya da ita babban Asibitin koyarwa na jihar inda a halin yanzu take samun kulawa.
A wata sanarwa, kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, ASP AbdulKareem Dungus ya ce jami’an su sun kama matashin.
A cewarsa, wayar da barawon ya kwace samfurin Itel ce hade da da layi a ciki.
Dungus ya ce za a ci gaba da bincike daga bisani a tura matashin zuwa kotu don fuskantar hukuncin da ya ya daidai da laifinsa, domin hakan zama izina ga na baya.