✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibi da iyayensa sun yi wa malamansa da firinsifal duka a Ogun

Iyayen sun je har makaranta suka lakada wa firinsifal da malaman dansu duka

Wani dalibin sakandare da iyayensa sun shiga uku bayan da suka je har makarantarsa suka lakada wa firinsifal da malamai duka a Jihar Ogun.

Dalibin da ke ajin karshe da iyayen nasa sun yi wa firinsifal da malaman duka ne saboda firinsifal din ya kwace masa inifom.

Wannan lamari ya faru ne a makarantar Agbara Grammar School da ke Karamar Hukumar Ado Odo-Ota a ranar Laraba.

Aminiya ta gano cewa dalibin ya yi rajistar jarabawar kammala sakandare ta WAEC da za a gudanar daga watan Mayu a wata makarantar kudi.

A sakamakon haka firinsifal din ya bukaci ya daina gabatar da kansa a matsayin dalibin makarantarsa, inda ya kwace inifom din dalibin.

Majiyar ta ce dalibin ya koma gida, kafin a jima, sai ya dawo tare da iyayensa, inda suka far wa firinsifal din da duka.

“Duk kokarin da aka yi na lallashinsu ya fasakra, inda suka kama firinsifal din da duka.

“Ana cikin haka ne dalibin ya gaura wa daya daga cikin malaman mari, ya yaga masa kaya,” in ji majiyar.

Ba za mu lamunta ba —Kwamishinan Ilimi

A kan haka ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Ogun, Farfesa Abayomi Arigbabu, ya lashi takobin hukunta dalibin da iyayensa.

“Ba zan lamunci irin wannan abin assha a makarantu ba; na riga na tuntubi duk mahukuntan da ya dace,  kuma ina tabbatar muku cewa daga dalibin har iyayensa sai sun girbi abin da suka shuka.

“Iyayen sun dawo suna ba da hakuri, amma na ce dole sai an kai su kotu.

“An saba samun dalibai da iyayensu sun hadu su doki malamai, amma tun watanni shida da suka gabata da aka yanke wa wasu iyaye hukuncin aikin hidimar al’umma na wata shida, ba a kara samu ba.

“Saboda haka su ma wadannan za gwamnatin jiha za ta gurfanar da su a kotu domin shi ne kadai yaren da masu kunnen kashi suke ji,” in ji Farfesa Arigbabu a ranar Lahadi.

A hukunta su —ASUSS

Shi ma Shugaban Kungiyar Malaman Makarantun Sakandare (ASUSS) na Jihar Ogun, Seun Agbesanwa, ya roki gwamnatin jihar ta tabbatar dalibin da iyayensa da duk masu hannu a harin da aka kai wa makarantar sun fuskanci hukunci.

Ana yawa samun dalibai sun kai wa malamansu hari a Jihar Ogun inda a watan yulin bara, gungun wasu daliban sakandare su 10 suka bi wani malaminsu suka lakada masa duka saboda ya hana su satar jarabawa a makarantar Isanbi Comprehensive High School da ke Ilisan-Remo a Karamar Hukumar  Ikenne.

A watan Oktoban 2021 kadai, akalla sau hudu aka samu daliban makarantun gwamnati sun kai wa malamansu hari.

Hakan hakan ya sa a lokacin gwamnatin jihar ta wajabta wa iyaye da dalibai sanya hannu a kan alkawarin rashin yin wannan dabancin.