Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Kaduna, sun gana da shugabannin al’ummar Kuriga da kuma iyayen daliban da aka sace a jihar.
Akalla daliban makarantar firamare da sakandare 300 ‘yan bindiga suka sace a kauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a jihar.
Sai dai Shettima ya bayar da tabbacin aniyar gwamnatin tarayya na ganin an ceto daliban.
Gwamna Uba Sani, Ministan Muhalli, Malam Balarabe Abbas, Kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Liman da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Ya shaida musu cewa shugaban kasa, ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da sun ceto daliban cikin kankanin lokaci.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya damu matuka kan sace daliban da aka a makon da ya wuce.
Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fama da hare-haren ta’addancin ‘yan bindiga.