✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a…

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki.

A cewar Gwamnan, bankuna da dama sun tunkare shi suna neman ya ci bashi amma ya ki saboda ba ya so ya ci gaba da dilmiyar da jihar a kangin bashi.

Gwamnan ya ce a maimakon haka, ya ma rage kudaden alawus-alawus na Sakataren Gwamnatin jihar da ma na Kwamishinoninsa domin ganin an rage facaka da kudaden gwamnati.

Ya ce, “Sakataren gwamnatina tsohon Babban Sakatare ne a gwamnatin tarayya, kuma tsohon ma’aikacin Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO). Wasu daga cikin Kwamishinonina kuna suna karbar albashi mai tsoka a wuraren aikinsu na baya.

“Hakan ne ya sa na roke su da su yi hakuri da wasu alawus-alawus din su sannan su yi amfani tsofaffin motocin da gwamnatin baya ta yi amfani da su. Haka muka yi muka ci gaba da tafiyar da gwamnatinmu ba tare da ciyo bashi ba ko daya ba,” in ji Uba Sani.