Jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama hakimin ƙauyen Guiwa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja.
Hakimin mai suna Garba Mohammed ana zarginsa da taimaka wa ’yan bindiga wajen aikata ta’addanci a yankin.
- Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai
- Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori
An kama shi tare da wasu mutum 13 a safiyar ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewar suna hannu wajen taikoman ’yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa hakimin yana bai wa ’yan bindiga mafaka a gidansa, inda suke taruwa suna shirya kai hare-haren.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa Aminiya kama hakimin ta wayar tarho.
Ya ce kama mutanen na daga cikin wani samame da ’yan sanda da ’yan sa-kai ke yi domin kawar da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Mashegu.
A ranar 22 ga watan Mayu, 2025, rundunar ta kai samame dazukan Magaman-Daji da kewaye, inda suka fatattaki masu aikata laifi.
A ranar 23 ga watan Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 9 na safe, rundunar ta sake afkawa ƙauyukan Guiwa da Telle bisa sahihan bayanai, inda aka kama hakimin Guiwa, Mallam Garba Mohammed, bisa zargin taimaka wa ’yan bindiga.
An gano babura huɗu da shanu 10 a gidansa, waɗanda ake zargin na ’yan bindiga ne.
Sauran mutum 13 an kama su a sassa daban-daban na Mashegu bisa zargin hannunsu a ta’addanci.
SP Abiodun, ya ce ana gudanar da bincike a kansu domin gano irin rawar da suka taka a ayyukan ta’addanci a yankin.
Ko da yake rundunar ba ta fitar da sunayen waɗanda aka kama ba, wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana sunayen wasu daga cikinsu.
Ya bayyana cewa akwai waɗanda suka fito daga ƙauyukan Wawa a Borgu, Gwajibo, Telle, Dukku a Rijau, Pallagi, Arera, Adogon Mallam da kuma Lumma.
Wani mazaunin New Bussa ya tabbatar wa Aminiya cewa an kama Alhaji Abdullahi Shehu daga Wawa da wasu mutum biyar daga Lumma.
Har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin.