✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: An ceto mutum 6 da dukiyar miliyan 107 a Kano

Hukumar ta ja hankalin mutane kan kula da ababen amfani na gida.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta sanar da ceto rayukan mutum shida da dukiyar Naira miliyan 107 daga gobara 74 da suka faru a watan Fabrairun 2024, a jihar.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Juma’a a Kano.

Abdullahi, ya kuma ce mutum hudu ne suka rasa rayukansu, yayin da gobarar ta kone dukiyar Naira miliyan 64.

“Mun samu kiran kai agaji bakwai daga kiran waya 10 daga mazauna jihar,” in ji shi.

Ya shawarci jama’a da suke kula sosai da abin da ya shafi wuta da lantarki.

Kazalika, ya ce wasu daga cikin gobarar sun tashi ne sanadin gas din girki.

Har wa yau, ya ce akwai bukatar mutanen jihar suke neman bayanai game da abin da ya shafi gobara da hanyoyin kare ta.