Wasu ‘yan banga a Jihar Ribas da aka fi sani da OSPAC sun kashe ‘yan uwan juna biyu — Collins Ugorji da Newman Ugorji — a yankin Idu da ke Ƙaramar Hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a jihar.
Ɗan uwan waɗanda aka kashe, Wade Ugorji, ya shaida wa wakilinmu a Fatakwal cewa, Collins da Newman sun je yankin Idu da ke jihar ne domin ziyartar ‘yan uwansu a lokacin da ‘yan bangar suka kama su.
Ya ce, jami’an tsaron sun zargi ‘yan uwansa a matsayin masu garkuwa da mutane, inda suka kai su sansaninsu suka harbe su har lahira.
Ya ce, ’yan banga sun tafi da wani babur mallakar waɗanda suka kashe da sauran kayansu.
Ya ce, “A ranar 1 ga Mayu 2024, ɗan uwana, Collins Ugorji wanda aka fi sani da NwaAba da kuma ƙaninsa Newman Ugorji, wanda ya fito daga Benin inda yake zaune, sun je unguwar Idu a Ƙaramar Hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a Jihar Ribas.
“Amma ya zuwa yammaci sai jami’an OSPAC sun kama su suka kashe su biyun kan zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.
“A ranar 2 ga watan Mayu ne muka ji labarin an kashe wasu masu garkuwa da mutane biyu a Idu, yayin da hotunansu ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta.
“Wani wanda ya gane su ne ya kira ni. Mun je ofishin ‘yan sanda na Omoku muka kai rahoton lamarin.
“Baturen ’yan sandan yankin da wasu jami’ansa da ƙannena biyu sun je unguwar Idu.
“Ɗaya daga cikin ‘yan Ƙungiyar ta OSPAC ya yi wa DPO ɗin barazana da cewa ba don yana riƙe da muƙamin DPO ba, da bai yi masa da sauƙi ba.”