A ranar Laraba ne jami’an Rundunar sojin ruwa ta Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas.
Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya yi karo da wani jirgin ruwa a tsakiyar kogin.
- Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara
- Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji
Jami’ar yaɗa labarai na sansanin, Laftanar Kwamanda Bridget Bebia, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, ta ruwaito Kwamandan sojojin masu aikin bincike, Commodore Cajethan Aniaku, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar Aniaku, ba a samu asarar rai ba, kuma an kuɓutar da akasarin kayayyakin fasinjojin tare da ceto su daga cikin jirgin.
Rundunar sojin ruwan ta ce jami’anta da ke NSS 035 tare da tallafin jiragen ruwa huɗu sun ƙaddamar da aikin bincike mai inganci, inda suka yi nasarar ceto dukkan fasinjoji 99.
“Saboda saurin agajin da tawagar ceto ta yi, ba a sami asarar rayuka ko jikkata ba,” in ji Rundunar Sojan Ruwa.