✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan yi musayar yawu da yara ba — Martanin Amaechi ga Wike

Tsofaffin abokan na siyasa biyu na ci gaba da musayar yawu a kafafen yaɗa labarai.

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin da ya sa ya naɗa Nyesom Wike a matsayin Shugaban Ma’aikata a lokacin da yake Gwamnan Jihar Ribas, maimakon Kwamishinan Kuɗi.

Amaechi, ya ce ya zaɓi Wike ne a matsayin Shugaban Ma’aikata domin ya samu damar sanya ido a kansa.

“Na so ya zama shugaban ma’aikata ne saboda na riƙa sanha ido a kansa.

“Ban ba shi kujerar kwamishinan kuɗi ba,” in ji Amaechi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise da yammacin ranar Talata.

Wannan martanin ya biyo bayan kalaman Wike ne, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya, inda ya yi martani kan wata magana da Amaechi ya yi a bikin cikarsa shekaru 60 a duniya.

Ya ce: “Dukaninmu muna jin yunwa.”

Wike ya ce Amaechi yana yunwarsa a fili kan lallai sai ya zama wani abu a siyasar Najeriya.

Sai dai Amaechi ya musanta zargin Wike na cewa shi ne ya taimaka masa ya zama gwamna.

“Ubangiji, tsohon gwamna Peter Odili, kotuna, da kuma al’ummar Jihar Ribas ne suka sa na zama gwamna,” in ji shi.

“Ka tambaye shi yadda ya sa na zama gwamna. Ina faɗin haka ne saboda bana so na yi musayar yawu da yara.”

Amaechi ya ƙara sukar Wike, inda ya ce a yanzu ba ya ganin girman kowa har waɗanda suka taimake shi a rayuwa.

“Ka ga shi ya naɗa kansa shugaban ma’aikata. Ya naɗa kansa gwamna. Ya yi wa kansa minista. Ya kuma yi wa kansa shugaban ƙaramar hukuma,” in ji Amaechi.

Amaechi ya ce bai ga amfanin yin cacar baki da Wike a bainar jama’a ba, domin hakan bai dace da shi ba.

“Ina faɗin haka ne saboda bana so na shiga cece-kuce da yara,” ya maimaita.

Rigima tsakanin tsoffin abokan siyasar biyu na ci gaba da jawo hankalin jama’a, musamman duba da tarihin siyasarsu a Jihar Ribas.