Mahara sun harbi wani dalibi sannan suka sace wasu kimanin 100 da firinsifal dinsu a wata makarantar gwamnati a Jihar Kaduna.
Da misalin karfe 8.30 na safiyar Alhamis ne mahara suka kai kutsa makarantar firamaren da ke hade da karamar sakandare a garin Kuriga a Karamar Hukumar Chikun.
Mazauna na fargabar daliban da aka sace sun kai dari, a makarantar wadda ke dalibai maza da mata, amma dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin ba.
Wani mazaunin garin Kuriga mai suna Lawal, ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun kora daliban da suka kama zuwa cikin daji, suka yi awon gaba da su.
- ’Yan Sa Kai Sun Yi Wa Limami Yankan Rago A Zamfara
- An tsare mutane 300 a gidajen yarin Kano ba bisa ka’ida ba —’Yan Sanda
Wani mazaunin garin mai suna Shitu kuma, ya ce da dama daga cikin daliban sun tsere bayan da suka ga shigowar mahara makarantar da ke wajen garin.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumanci daga ma’aikatar ilimi ko ta tsaron Jihar Kaduna kan lamarin, duk da cewa wakilinmu ya aika wa kwamishina tsaro, Samuel Aruwan, sako domin neman karin bayani.
Haka zalika kokarin wakilinmu na samun bayani daga kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya faskara.