’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara.
Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar.
Wani jami’in gudanarwa na makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun shiga harabar makarantar ne ta wata ƙofa da ke bayan katangar makarantar.
“Sun mamaye harabar makarantar sanye da cikakkun kayan ’yan sanda, da hula da takalman roba. Sun yi amfani da kofar da ke bayan katangar wajen shiga da kuma guduwa bayan harin,” in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe malamin ne a lokacin da yake ƙoƙarin turjewa.
“Ya fuskanci ’yan bindigar har ma ya yi nasarar rinjayar ɗayansu kafin a harbe shi har lahira,” kamar yadda majiyar ta bayyana.
Daga bisani maharan sun sace matar malamin da wasu mata biyu a lokacin harin.
Shaidu daga ma’aikatan makarantar sun bayyana cewa, “Ƙarar harbe-harben bindigar da ya ɓarke ya sa ɗalibai suka fara ihu ‘ɓarayi,’ wanda da farko ya sa wasu ma’aikata zaton ƙaramar sata ce. Sai dai, yawan harbe-harben da aka yi a jere ya kawar da wannan zaton,” in ji wani ma’aikaci.
Ya ƙara da cewa ’yan sanda da sojoji sun isa wurin ne bayan maharan sun riga sun gudu.
“Babban ɗan sanda na yankin (DPO) ya taimaka wajen kai gawar malamin gidansa da ke cikin gari domin shirye-shiryen jana’iza,” kamar yadda majiyar ta ƙara bayyanawa.
Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, kwanan nan ta sauya tsarin karatunta zuwa ne je-ka-ka-dawo saboda rashin tsaro da ya addabi yankin.
Ma’aikatan makarantar sun tabbatar da cewa, “Wannan shi ne karo na farko da aka kai mana hari. Mutanen yankin sukan zo nan don shakatawa,” in ji wani ma’aikaci cikin baƙin ciki.
Tagwayen hare-hare a Zamfara
Wannan harin da aka kai makarantar ya zo daidai da jerin hare-hare da ’yan bindiga suka kai a wasu ƙananan hukumomi da dama a Jihar Zamfara.
A Ƙaramar Hukumar Anka, an ruwaito cewa ’yan bindiga sun sace mata biyu da yara shida na wani magidanci Abdullahi Azee.
A ƙauyen Madira da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, an kashe mutane biyu.
Bugu da ƙari, a Damba da ke Ƙaramar Hukumar Gusau, an sace wani mutum da matarsa, da jaririnsu ɗan wata huɗu.
A halin da ake ciki, a Ƙaramar Hukumar Maru, ƙoƙarin da aka yi na mamaye ƙauyen Kadauri ya ci tura sakamakon haɗin gwiwar ’yan banga na yankin da jami’an tsaro, wanda ya tilasta wa maharan janyewa.
Jihar Zamfara ta ci gaba da zama cibiyar ayyukan ’yan bindiga da satar mutane a ’yan shekarun nan, duk da ƙarin yawan jami’an tsaro da aka tura.
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da harin da aka kai makarantar.
Ya ba da tabbacin cewa zai yi bincike domin tabbatar da bayanan sannan ya ba da amsa.
Sai dai, har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labarin, ba a samu wani ƙarin bayani daga rundunar ’yan sandan ba.