Wasu ’yan tireda masu tura baro a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano sun yi zanga-zangar adawa da korarsu da aka yi daga kasuwar.
Aminiya ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar na zargin Shugaban Kasuwar, Abdul Bashir Hussain da tilasta musu barin kasuwar.
’Yan baron sun yi ƙorafin cewa wannan kora da aka yi musu ta kai matakin zama abin barazana ga rayuwarsu.
- An bukaci Tinubu ya bayar da umarnin kuɓutar da ɗan jaridar da aka sace a Legas
- Tinubu na halartar jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Delta
Da yake jawabi, jagoran masu zanga-zangar wanda shi ne Sakataren Ƙungiyar ’Yan Baro, Sanusi Sale Abdallah, ya bayyana cewa duk da sun sallama wa duk wasu sauye-sauyen da suka dace, amma mahukuntan kasuwar sun dage kan korar su.
“Ana gama rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasuwa ya gaya mana cewa ba ya son ganinmu a kasuwa.
“Mun gabatar masa hanzarin cewa za mu yi biyayya ga duk sabbin tsare-tsare amma har yanzu ya nace cewa dole ne sai mun bar kasuwar.
“Mu ’yan asalin Jihar Kano ne masu biyayya ga Gwamna Abba Kabiru Yusuf. Saboda me wannan sabon shugaban kasuwar yake yi mana haka, don haka ba ma yi.”
Aminiya ta tuntubi Shugaban Kasuwar, Abdul Bashir Hussain, inda ya tabbatar da korar ’yan baron daga kasuwar.
A cewarsa, sana’ar da suke yi a tsakiyar hanya tana rufe tituna a kasuwar wanda hakan ke kara tsananta cunkoso kuma cudanya tsakanin maza da mata tana karuwa a kasuwar wanda hakan ya ci karo da koyarwar addinin Musulunci.
Ya ce hukumar ta ba su shawarar fitar da baron nasu daga kasuwa amma sun dage lallai sai sun yi amfani da su wanda hakan ya sa aka kore su.
Sabon shugaban kasuwar ya kara da cewa har yanzu suna da kudirin sake tsugunar da su a wani wurin na daban domin ci gaba da sana’o’insu.