✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci Tinubu ya bayar da umarnin kuɓutar da ɗan jaridar da aka sace a Legas

‘Yan jarida da masu kare haƙƙin bil’adama a duniya sun shiga fargaba kan sace dan jaridar da aka yi.

An bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da karfin ikon ofishinsa na babban kwamandan tsaro domin bayar da umarnin kuɓutar da ɗan jaridar nan Segun Olatunji da ake dauke a Jihar Legas.

Kwamitin Cibiyar Yaɗa Labarai ta Kasa (IPI Nigeria) ne ya yi wannan kira na neman shugaban kasar da ya bai wa babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa umarnin kubutar da wakilin jaridar FirstNews da aka sace a gidansa kwanaki 12 da suka gabata.

A ranar 15 ga Maris, wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan Olatunji da ke Iyana Odo a unguwar Abule Egba ta Jihar Legas, inda suka yi awon gaba da shi.

Yayin da iyalan ɗan jaridar ba su samu wata sanarwa daga waɗanda suka dauke shi ba, mahukuntan kafar yaɗa labaran sun danganta lamarin da wani rahoto na baya-bayan nan da FirstNews ta wallafa.

Sai dai IPI ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa dan jaridar na hannun sashen leƙen asiri na hedikwatar tsaron Najeriya DIA, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, wanda ta ce dole ne ya yi wa babban hafsan tsaron ƙasa Janar Musa biyayya.

“Kwanaki goma sha ɗaya da suka gabata, ɗan jaridar da aka sace an tsare shi ba tare da sanin inda yake ba. Ba tare da sanin iyalansa, ma’aikatansa, da abokan aikinsa ba, duk ba su san inda yake ba.

“IPI Najeriya ta karbi korafe-korafe da neman karin bayani game da wannan batu daga ko’ina a fadin duniya.

“Cibiyar ta kuma tuntuɓi rundunar ‘yan sanda da sojojin Najeriya, da hukumar leƙen asiri ta hedikwatar tsaro, da hedkwatar tsaro, da ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta ƙasa, inda suka buƙaci a sake shi. Duk ƙoƙarin da aka yi a wannan ɓangaren ya ci tura ya zuwa yanzu.

“Hakan ya jawo fargaba a tsakanin ‘yan jarida da masu rajin kare haƙƙin bil’adama a duniya da zargin cewa sojojin Najeriya na iya boye wasu muhimman bayanai da suka shafi lafiyar ɗan jaridar.