’Yan bindiga kimanin 40 sun bakunci lahira a hannun ’yan banga a yankin Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
A ranar Asabar din makon shekaranjiya ’yan bana suka yi nasarar aika ’yan bindigar lahira a wata arangama a tsakaninsu a Dajin Katakaki da ke yankin.
Aminiya ta gano cewa ’yan banga 19 sun kwanta dama a yayin musayar wutar da aka yi kimanin kwanaki 10 da suka gabata.
Akalla sama ’yan bindiga 40 ne aka ruwaito sun mutu a arangamar a lokacin da ’yan bindigar suka kai harin a yayin da jama’ar yankin suke aiki a gonakinsu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani shugaban matasan yankin mai suna Shehu Randagi, ya sanar da cewa an gano gawarwakin ’yan bindiga 19 a cikin daji, sauran da suka jikkata kuma sun kwashe ragowar gawarwakin domin kada a gane su.
“Arangama ce da aka zubar da jini wanda ’yan banga 19 suka mutu, wasu biyu kuma suka bace. Mun kuma gano gawarwaki 19 na ’yan bindiga a dajin Katakaki.
“Mutanen kauyen Dogon Dawa Daji da ke kusa da iyakar Jihar Neja, sun sanar da mu cewa, sun ga gawarwakin ’yan bindiga sama da 40 da sauran maharan suka diba a kan babura bayan arangamar,” in ji shi.
Shehu Randagi ya jaddada cewa mazauna yankin ne suke kare kansu daga ’yan ta’adda, domin babu jami’an tsaro a kudancin Birnin Gwari.
Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa ’yan bindigar sun yi asarar rayuka da dama.
Ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki kan mutanen kauyen ne a lokacin da suke aikin gona, amma ’yan banga suka yi artabu da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka daga bangarorin biyu.
Ya kuma ce an kuma lalata manyan motoci da amfanin gona a yayin arangamar.
Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan.