✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DAGA LARABA: Ina Aka Kwana A Binciken Harin Tudun Biri?

Wata guda bayan kai harin, shin an fara bincike kuwa?

More Podcasts

Yanzu wata guda ke nan tun bayan da jirgin sojoji ya yi kuskuren kai hari kan masu taron Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin da kuma bayyana matakan da za a bi wajen kwato hakkin waɗanda lamarin ya shafa.

Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina kudaden da aka tara na tallafi suke?

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari na musamman a kan matakin da ake kai na bincike kan harin.

Domin sauke shirin, latsa nan