Jama’ar kauyen Tudun Biri da jirgin sojojin Najeriya ya yi wa ’yan uwansu luguden wuta a wurin taron Maulidi sun buƙaci a tabbatar da an hukunta duk wanda bincike ya nuna da hannunsa harin.
Imam Aliyu Nyass, ɗaya daga cikin shehunnan yankin, ya bukaci a aiwatar da sakamakon binciken kwamitin da Rundunar Sojin Najeriya ta kafa domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Yayin tattaunawar wakikinmu da malaman addinin da wasu masu ruwa da tsaki da iyayen waɗanda da abin ya shafa, jama’ar garin da jirgin sojojin saman Najeriya ya hallakawa kusan mutane 100 ta zamo guda — Dukkansu sun yi kira ne da a yi adalci ga wadanda abin ya shafa.
A ranar Alhamis ne dai daraktan yaɗa labaran Hedkwatar Tsaron Najeriya, Manjo-Janar Edward Buba, ya bayyana cewa an kammala binciken da aka kwashe watanni ana yi.
Edward Buba ya ce sakamakon binciken ya nuna cewa akwai lauje cikin naɗi, kuma an samu wasu sojoji da laifin kai harin na ganganci.
- Harin Tudun Biri: Sojoji Sun Yi Ganganci —Hedikwakar tsaro
- An kama wanda ya kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
Imam Nyass ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar Kaduna da su dubi girman Allah su cika alƙawarin da suka yi wa jama’ar da abin ya shafa.
Imam ya ce, “Tun bayan faruwar lamarin nan, an yi alƙawarin gina mana gidaje da asibiti da hanya, amma har yanzu babu abin da aka fara dangane da gidaje da asibiti, an dai ɗan share hanyarmu kaɗan.”
Malam Bello Tudun Biri, wani mazaunin garin wanda ’yarsa ta samu rauni a harin, ya bayyana jin dadinsa kan yadda rahoton ya bayyana an samu wasu sojoji da laifi.
Kamar Imam Nyass, Bello ya roƙi a yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.
Ya kuma jaddada cewa idan duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukuncin laifin da suka aikata, hakan zai hana wasu yin irin hakan a gaba.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta cika alkawuran da ta yi wa iyalan waɗanda abin ya shafa.
A cewarsa, har yanzu ba a cika alkawarin samar da gidaje da asibitoci a yankin ba.
Auwal Ugara, mahaifin wani matashi aka kashe a harin, ya yi kira da a yi wa ɗan nasa adalci.
Ya bayyana cewa, tun bayan faruwar lamarin, har yanzu ba a biya su diyya ba, inda ya ce dansa yana makarantar sakandare kafin rasuwarsa.