Gwamnatin Tarayya ta kira taron tattaunawa da shugabannin kungiyar kwadago (NLC da TUC) wadanda suka fara yajin aikin sai abin da hali ya yi.
Tun a ranar Litinin gwamnati ta gargadi shugabannin kungiyar kwadago kan shiga akin aikin, tana mai jan hankalinsu kan umarnin kotun ma’aikata da ya hana su shiga yajin aikin.
A yau Talata Ministan Kwadago, Simon Lalong, zai jagoranci taron bayan kungiyoyin da ke karkashin inuwar NLC sun tsunduma yajin aikin da safe a bisa umarnin NLC na ranar Litinin.
Shugaban kungiyar ma’aikata ta TUC, Festus Osifo ne ya sanar da shigarsu yajin aikin a Abuja, yana mai cewa ba za su dawo aiki ba, sai gwamnati ta yi dukkan abin da ya kamata.
- Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 bayan saukarsu a Jidda
- Gidajen mai sun kara kudin lita zuwa N640 a Abuja
Shugaban NLC da Rikicin Imo
Yajin aikin bore ne bisa dukan da aka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero da wasu manyan jami’ansa a Owerri, Jihar Imo, kan wasu bukatun ma’aikata.
Kakakin NLC, Benson Upah, ya ce a ranar 1 ga watan Nuwamba ’yan sanda suka tsare Ajaero gabanin zanga-zangar da NLC ta kira a Jihar Imo domin neman biyan bukatun ma’aikata.
Rundunar ’yan sandan jihar ta musanta zargin, inda ta ce ta ajiye shi ne a matsayin kariya daga kai masa hari.
A bangare guda kuma gwamnan jihar, Hope Uzodinma ya zargi shugaban na NLC da tsoma baki a siyasar jihar.
Daga bisani NLC da TUC suka rubuta umarci rassansu — kungiyoyin malaman jami’a da na ma’aikatan lantarki da na malamai da na ma’aikatan shari’a da na kwalejojin da sauransu — cewa su shirya shiga yajin aiki.
Wasakiyar mai dauke da sa hannun Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja da takwaransa na TUC, Nuhu Toro ta ba kuma wa kungiyoyin kwadago a matakin jihohi umarnin fara yajin aikin daga safiyar Talata, har sai abin da hali ya yi.
NLC ba ta kyauta ba
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana yajin aikin a matsayin neman zagon kasa ga gwamnati da wuce gona da iri da kuma bijire wa umarnin kotun ma’aikata da ta hana shiga yajin aikin.
Hadimin shugaban kasa kan yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya ce yadda aka yi wa Ajaero a Imo abin Alla-wadai ne, amma duk da haka bai kamata kungiyar ta yi amfani da shi ta je da daukacin ’yan Najeriya cikin wahala ba.
Ya ce babu dalilin NLC ta saba umarnin kotu, alhali shugaban ’yan sandan Najeriya ya ba da umarnin bincikar lamarin har ya sauya wa kwamishinan ’yan sandan Imo wanda abin ya faru a karkashin ikonsa wurin aiki daga jihar.
A cewarsa, ba daidai ba ne ’yan kungiyar kwadago su rika amfani da ita domin biyan bukatunsu na kashin kai, ballantana har ta kasance mai karya dokar kasa da saba umarninn kotu.
Onanuga ya ce fitar da sanarwar yajin aikin bayan tashi aiki a ranar Litinin ya nuna cewa an kitsa shi ne domin hana ruwa gudu.