✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami ƙarin ma’aikata 639 a tashar Muryar Amurka

An sallami ma'aikata 1,400 a kafar yaɗa labaran, a wani ɓangare na shirin Shugaban Amurka Donald Trump na rage ma'aikata

Gwamnatin Amurka ta kori ’yan jarida da wasu ƙarin ma’aikata 639 da ke aiki a kafar yaɗa labarai ta Muryar Amurka (VOA) a ranar Juma’a.

Hukumar Kula da Harkokin Watsa Labarai ta Duniya ta Amurka (USAGM) ta bayyana cewa kawo yanzu an sallami ma’aikata 1,400 a wani bangare na shirin Shugaban Amurka Donald Trump na rage ma’aikata a hukumar zuwa mafi ƙarancin adadi kamar yadda doka ta tanada.

Hakan na nufin an kori mutum takwas a cikin kowane ma’aikata 10 da ke VOA a wata uku da suka gabata, a sakamakon wannan matakin Hukumar USAGM ta ɗauka.

Babbar Mashawarciya ga Hukumar, Kari Lake, ta bayyana cewa, “An aika wa ma’aikata 639 a VOA da USAGM da takardun kora a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da ya kamata a yi tun da daɗewa don kawar da dimbin ma’aikata cima-zaune da kuma rashin riƙon amana a hukumar,” in ji sanarwar da ta fitar.

Kari Lake ta kuma tabbatar da cewa hukumar ta kasance “cike da jami’an da ba sa aiki komai, nuna son kai, da ɓarnatar da dukiya.”

Ta bayyana cewa wannan mataki na nufin USAGM yanzu tana aiki kusa da mafi ƙarancin ma’aikata 81 da doka ta tanada.

Ma’aikata 250 kuma za su ci gaba da zama a Ofishin Watsa Labarai na Cuba (OCB), wanda ke watsa labarai zuwa ƙasar Cuba mai mulkin kwaminisanci.

An lura cewa babu ko ɗaya daga cikin ma’aikata 33 na OCB da aka kora.

Wannan mataki mai yiwuwa alama ce ta kusan kawo ƙarshen wannan shahararren gidan rediyo VOA wanda miliyoyin mutane ke saurara tsawon shekara 50 a faɗin duniya.

VOA, wadda aka kafa a 1942 don yaƙar farfagandar Nazi, tana watsa shirye-shirye a kusan harsuna 50 kuma ta mutane miliyan 360 ke sauraron shirye-shiryenta a mako, a faɗin duniya.

A watan Mayu aka kori ma’aikatan kwangila kusan 600 na VOA.

Wasu ’yan jam’iyyar Republican a baya sun zargi tashar da sauran kafofin yaɗa labarai masu samun tallafin gwamnati da nuna son kai ga masu ra’ayin mazan jiya, suna masu kira da a rufe tashar a matsayin wani ɓangare na rage kashe kuɗin gwamnati.

Wata tashar USAGM, Radio Free Asia, wadda tuni aka rage ma’aikatanta sosai, ta sanar a cikin wani sakon imel ga ma’aikata a ranar Juma’a cewa tana aiwatar da karin hutun tilas a sassa daban-daban.

Ana ci gaba da shari’o’i daban-daban kan lamarin korar ma’aikatan na USAGM.