✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 bayan saukarsu a Jidda

Gwamnatin Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 da suka je Umrah a daidai lokacin da Tinubu ke ziyarar aiki a kasar

Gwamnatin Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriya 264 da suka je Umrah a daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke ziyarar aiki a kasar.

Saudiyya ta soke bizar daukacin ’yan Najeriya 264 da suka je kasar daga Kano da Legas ne, ta kuma ba da umarnin a dawo da su gida ne a ranar Lahadi.

Saukar jirgin kamfanin Air Peace da fasinjojin ke da wuya a Jiddah, jami’an filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz suka samu sanarwar cewa an soke bizar daukacin fasinjojin da suka iso daga Najeriya.

Kafin barin Najeriya sai da aka yi wa fasinjojin tantacewa da binciken kwakwaf a filayen jirgi, da sanya idon hukumomin Saudiyya kuma aka tabbatar cewa bizarsu ba ta da matsala.

Hakan ta faru ne a yayin da Shugaba Bola Tinubu da kusoshin gwamnatinsa suke halartar taron tattalin arzikin kasahen Larabawa da Afirka a Saudiyya, inda kuma suka yi Umrah.

Kimanin makonni biyu ke nan da Air Peace ya fara jigijalar fasinjoji kai-tsaye daga Najeriya zuwa Jidda.

“Muna zargin wannan wani shiri ne na sanya hakar fita a ran kamfanin, saboda akwai wadanda ba su ji dadin fara aikin Air Peace kai tsaye daga Najeriya zuwa Jidda ba, sabanin kamfanonin jiragen kasashen waje da suka fi shi tsada,” in ji wata majiya.

Aminiya ta gano daga bisani Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya ya rage adadin wadanda za a dawo da su gida zuwa 177, wadanda yawancinsu su tafi Saudiyya ne domin yin ibadar Umrah.

Kafin fara tashin Air Peace kai tsaye zuwa Jidda, kamfanin Saudiyya na yin wannan aiki.

%d bloggers like this: