✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan matan Jigawa ke ɗinkin huluna don dogaro da kansu

Wata mai suna Zainab ta ce tana alfahari da wannan sana’a domin ba ta jira saurayinta ya sayo mata kaya.

Wasu ’yan mata a Jihar Jigawa sun samu hanya ta musamman ta dogaro da kansu ta yadda za su ƙarfafa tattalin arzikinsu ta hanyar yin sana’ar ɗinkin huluna da ake kira Zanna Bukar ko Kofar ko Kanwa da sauransu.

Wannan sana’a ta gargajiya ta zama abin alfahari ga ’yan mata da dama a jihar.

Sai dai ’yan mata da matan aure a yankin Andaza da ke Ƙaramar Hukumar Kiyawa da ke jihar ne suka yi fice a wannan sana’a inda suke zama a cikin gidaje ƙungiya-ƙungiya suna ɗinkin hulunan.

Ana amfani da huluna a Ƙasar Hausa a matsayin ado na lal’ada kuma ana ɗaukarsu a matsayin muhimmin sashe na kayan gargajiya.

Waɗannan mata da ke yin wannan sana’a sun ce sun samu ci gaba a kuɗin da suke samu daga sana’ar wadda ke ba su damar samun ’yancin dogaro da kai, saboda suna samun abin rayuwa da kuma tallafa wa danginsu ta hanyar saƙar hula.

Bugu da ƙari, sana’ar ta taimaka musu wajen adana abubuwan al’adun yankin, saboda maza suna jin ba su cika ba tare da sun kai ƙololuwa ba ta fuskar sanya tufafin gargajiya.

Yana da kyau a lura cewa waɗannan huluna da ake yi a gida ba kawai game da ƙarfafa tattalin arziki ba ne har ma da kiyaye al’adun gargajiya na Arewacin Nijeriya.

Wata mai ɗinkin hular mai suna Amina Sani, ’yar shekara 17 daga Andaza a Ƙaramar Hukumar Kiyawa ta ce sana’ar ta kawo mata arziki saboda ta sayo kayayyaki da dama da suka haɗa da awaki, kayan gyara da sauransu.

Haka nan tana tallafa wa iyayenta daga kuɗi, amma a cewarta, ƙalubalen da suke fuskanta ita ce ta hauhawar farashin kayayyakin ɗinki da tsadar sauran kayayyaki.

Sai ta ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa mutane wajen magance matsalar.

Wata ’yar shekara 19 mai suna Hauwa Hamisu da ke ƙauyen Andaza ta ce ta rungumi wannan sana’a ce sakamakon rashin sana’ar da ta fi samun riba wacce za ta kawo mata kuɗi fiye da yin kwalliya.

Hauwa Hamisu ta ce takan gama hula ɗaya a cikin mako huɗu ko kuma mako uku idan ta rage yawan aiki.

Daga nan sai ta koka cewa kayan ɗinki sun yi tsada duk da cewa farashin hular bai kai haka ba, domin ana sayar da ita a tsakanin Naira 7,000 zuwa Naira 8,000 ne kawai.

Ta yi kira ga gwamnati ta dubi matsalar talakawa a wannan mawuyacin lokaci.

Ummulkhairi Ja’afar ita ma mai ɗinkin hula ’yar unguwar ce, ta ce a lokacin da take sayar da hulunanta a Kasuwar Shuwarin, daga kuɗin da aka samu take sayan kayan gida da kayan kwalliyarta kafin aurenta.

A cewarta, suna sayar da hula a Kasuwar Shuwarin tsakanin Naira 7,000 zuwa 8.000 duk da tsadar kayan ɗinki da tsadar rayuwa.

Wata mai suna Zainab Isah da ta kasance tana ƙarasa hula a cikin mako guda ta ce ta fara koyon yadda ake ɗinkin hular ce tun tana ’yar shekara shida.

Zainab ta ce tana alfahari da wannan sana’a domin ba ta jira saurayinta ya sayo mata kaya.

Daga nan sai ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su tallafa musu da kayan aiki domin ƙara inganta sana’arsu.

Malam Musa Isma’il, wani mai sayar da kayan ɗinkin huluna a Unguwar Sha’iskawa da ke cikin birnin Dutse, ya ce sana’ar ɗinkin hula babbar sana’a ce ta mata a Arewacin Nijeriya yayin da wasu suka ƙware wajen zanen hular.

Isma’il ya ce matsalar da suke fuskanta ita ce ta hauhawar farashin kayayyakin da ake amfani da su wajen yin ɗinkin hula domin kusan kowace rana farashin yana ci gaba da hauhawa.

Ya ce mata su ne manyan kwastomominsu kuma ba sa son ƙarin farashin kowane kaya.

Ya yi kira ga gwamnati ta kafa kamfanonin yin kayan da ake buƙata wajen ɗinka huluna a Nijeriya waɗanda za su riƙa samar da kayan ɗinkin hula a cikin gida domin kusan dukkan kayayyakin ana shigo da su ne daga waje.