✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tsohuwa ta sace lu’lu’un biliyan N2.4

Ta yi satar a wani katafaren shagon sayar da duwatsu masu daraja.

An cafke wata tsohuwa da ta sace lu’ulu’u na Fam miliyan 4.2 (kimanin Naira biliyan 2.4) tare da maye gurbinsu da duwatsu.

Lulu Lakatos, mai shekara 60 ta sace lu’ulu’un ne bayan ta yi shigar burtu a matsayin masaniyar duwatsu masu daraja a wani katafaren shagon sayar da duwatsu masu daraja, mai suna Boodles a birin London a kasar Birtaniyya.

Bayan ta yi wa lu’ulu’un bakwai kallon tsanaki, ta kimatanta kudinsu, sai ta mayar da su a cikin wata karamar jaka ta ajiye.

Daga baya da aka bude jikar sai aka ga duwatsu guda bakwai, kamar yadda mai shigar da kara, Philip Schott ya shaida wa kotun Southwark, yayin gabatar da tsohuwar da satar lu’un ta hanyar yin suddabaru.

Ya ce daga baya Mis Lakatos, ta shiga gidan wanka inda ta bar hularta da mayafin da take sanye da su, ta kuma samu wani abokinta da ta ya taimaka mata ta canza kaya, daga nan ba ta tsaya ko’ina ba sai filin jirgin sama, ta fice daga Birtaniya zuwa kasar Faransa.

Scott ya ce daga, “Abin da ta aikata ya kai matuka wajen shiri da daukar kasada domin samun lada”, amma tsohuwar ta musanta laifin da ake zargin ta da aikatawa.

– Abin da ya faru –

Tsohuwar ta je Boodles ne a matsayin wakiliyar wasu attajirai da za su sayi lu’ulu’un, inda za ta tabbatar musu da nauyinsu da kimarsu kafin a biya kudin.

An yi ganawar da ita ne bayan masu sayen sun yi zama da Shugaban Boodles, Nicholas Wainwrights, inda suka bayyana mishi muradunsu na yin sayayyar daga kamfanin nasa.

A nan ne suka umarci Lulu Lakatos, wadda suka kira da suna Ana, cewa ta je ta tabbatar da ingancin lu’ulu’un kafin su tura kudin.

Bayan zuwanta ofishin, masananin duwatsu masu daraja na Boodles inda ta rika duba lu’ulu’un daya bayan daya.

Duk wanda ta gama dubawa sai ta mayar cikin takardun da aka tanadar na musamman sannan ta sanya su a cikin wata karamar kwali mai duhu.

“Bayan kammalawa sai aka sanya kananan kwalayen a cikin wata karamar jaka mai zif, aka kulle da kwado,“ kamar yadda Scott ya shaida wa kotun.

Mai shigar da karar ya ce Mis Lakatos ta sanya karamar jikar a cikin jakarta ta hannu bayan da Mista  Wainwright ya hau saman bene.

“Ba mamaki an musayar jakar da aka kulle ne da wata irinta,” inji shi.

Ya ce daga baya sai Mis Lakatos, ta shiga gidan wanka inda ta jefar da hularta da mayafin da take sanye da su.

A gidan wankan ne kuma wani abokinta ya taimaka mata ta sauya doguwar rigar da ta sanya mai duhu ta sanya wata mai haske.

Daga nan ba ta yi wata-wata ba wajen ficewa daga birnin London zuwa inda take da zama Faransa, kafin daga baya a cafko a mayar da ita Birtaniya domin fuskantar hukunci.

A halin yanzu dai an dage sauraron shari’ar.