Rufe makarantu da nufin hana yaduwar cutar coronavirus na iya kawo karuwar daukar ciki da zubar da shi da kuma daina karatu a tsakanin ’yan mata, a cewar Hukumar Kula da Yawan Al’umma ta Najeriya (NPC).
Mukaddashin shugaban hukumar, Tayo Oyetunji, wanda ya bayyana haka, ya kuma ce zaman gida ya kawo karuwar cin zarafin mata da suka hada da fyade da dangoginsa.
“Idan ba a zuwa makaranta ’yan mata da dama na iya daina karatu, baya ga sauran illoli kamar auren wuri, saurin haihuwa da mace-mace sanadiyyar cututtuka ko haihuwa da kuma zubar da ciki da rashin ganin kimar kai”, inji shi.
A jawabinsa na Ranar Yawan Al’umma ta Duniya ta 2020, shugaban hukumar ya ce dokar kulle ta kara tsananta matsalolin da mata da ’yan mata ke fama da su na karancin kayan kula da lafiyar haihuwa.
“COVID-19 ya sa mata na shan walahar samun kula da lafiyarsu ta haihuwa, musamman saboda rashin abun hawa da kuma matsin da ke kan cibiyoyin lafiya”, kamar yadda ya ce.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta dakatar da bude makarantu ga dalibai masu jararbawar kammala sakandare saboda gudun karuwar masu cutar coronavirus a Najeriya.
Taken ranar yawan al’umma ta bana shi ne Kare Lafiya da ’Yancin Mata da ’Yan Mata ta Hanyar Magance COVID-19.