✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi

An buɗe wa matan wuta ne a lokacin da kowacce daga cikinsu ke tsaka da kula da gonarta.

Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta.

An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su har lahira.

“Mun yi tunanin za mu ɗauko su da rai ne lokacin da muka samu labarin a ranar Laraba, amma sai muka iske gawarwakinsu an yi musu ruwan harsasai da kuma ƙuna a jikinsu.