✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikici tsakanin Hausawa ya ci ran magidanci a Abeokuta

Abokin mamacin mai suna Mukhtar ya ce an kashe mamacin ne a kan wayar salula.

A ranar juma’ar da ta gabata ce, al’ummar garin Sabo Abeokuta da ke Jihar Ogun suka wayi gari da labarin kisan gillar da wasu mutane suka yi wa wani mutum mai suna Muhammadu Mustapha a daren ranar, bayan da suka yi ta dukansa har ya mutu, sannan suka kwashe ‘yan kwamatsansu suka gudu, suka bar garin, tun kafin gari ya waye.

Sarkin Hausawan Abeokuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan wanda ya jagoranci yi wa mamacin sutura a makabartar garin Sabo Abeokuta a ranar Juma’ar da ta gabata, ya shaida wa Aminiya cewa, tun a daren da aka yi kisan da misalin karfe dayan dare wasu mutane sun zo gidansa suka shaida masa cewa fada ya barke.

“Na yi mamaki ganin yadda suka zo cikin daren suna buga min kofa, sai na ce masu tunda fada ake ku kai wa ‘yan sanda rahoto.

“Nan na bukaci da su tafi wajen ‘yan sanda su sanar da su, ko da garin Allah ya waye sai muka iske ashe fada ne ya kaure a kan waya, har ta kai ga kisan kai,” in ji shi.

Ya ce, magidancin da aka kashe da wadanda suka yi kisan duk ‘yan gari guda ne, “dukansu ‘yan garin Jahun ne a Jihar Jigawa, wadanda suka hada kai suka yi kisan duk a daki guda suke zaune, wato wani dakin kwano a saman kwangirin jirgi.

Daya daga cikin masu yin kisan ne ya yi zargin cewa wata karamar waya da ya gani a hannun mamacin tasa ce, shi kuma mamacin ya ce ba ta shi ba ce, a kan wannan ne sai shi wanccan da abokansa suka rufe mamacin da duka, har ta kai ga sun yanke shi da wuka, kuma hakan ya yi ajalinsa.

Bayan sun yi aika-aikar duk sai suka gudu tun a cikin daren, daman ire-iren wadannan miyagun matasa da ke zuwa nan kudu ci-rani suna ta da tarzoma ba su da komai, ba su ajiye komai ba, daga su sai tsummokaransu a leda, wanda da zarar sun ta da tarzoma ko rikici sai su dauki kayansu a leda su gudu.

“Yanzu da wannan mutum da aka kashe Bayarabe ne, da yanzu sun jaza mana, sun gudu sun bar mu da wahala, don haka na ba da umarnin a rushe duka rumfuna da dakunan da suke zaune, dama wuri ne suka share suke zaune kara zube, suna aikata masha’a.

“Yanzu na ba da imarnin a rushe wajen na kuma kori kowa daga wajen domin ba za mu laminci wasu su zo su tada mana da hankali ba, kuma ina kira ga duk wani dan Arewa da ke zuwa ci-rani Kurmi ya guji ta da tarzoma, ya zo ya nemi arziki, amma ya guji fitina, domin Allah Ya la’anci duk wani mai ta da fitina” in ji shi.

Sarkin Hausawan ya ce, ‘yan sanda sun kama wasu da ake zargi da alaka da rikicin, ya ce duk wanda binciken ‘yan sanda ya tabbatar ba shi da laifi za a sallame shi.

Aminiya ta zanta da wani abokin mamacin mai suna Mukhtar, wanda ya ce an kashe mamacin ne a kan wayar salula, inda ya ce Mustapha na zaune a shagonsa sai ya bukaci wani yaro mai sayar da shayi da ya dafa masa taliyar indomi, “ko da yaron ya kawo masa taliyar, sai ya ga wayar Mustapha a kan tebur sai ya ce ai tasa ce.

“Mustapha ya ce ba ta sa ba ce, nan yaron ya je ya dawo da abokansa suka zo wajen suka rufe Mustapha da duka har suka kashe shi.

“Ni na san Mustapha da wannan wayar fiye da shekara biyu, amma yaron an sace masa waya ne cikin kwana biyu, shi ne ya zo ya ta da wannan tarzoma, yanzu haka iyalin wanda aka kashe, wato matarsa da karamin dansa suna nan cikin rashin lafiya sakamakon wannan tashin hankali.

“Marigayin ya bar mace guda ne da da guda, muna fatan za a yi masu adalci a bi hakin mamacinsu da aka kashe” in ji shi.

“A lokacin tarzomar an yi ta yada jitajitar cewa masu tuka babur na acaba ne suka ta da tarzomar, sai dai a hakikanin gaskiya, da wanda aka kashe da wadanda suka yi kisan babu wani mai sana’ar acaba,” a cewar Adam Ramat Usman, wanda dan acaba ne kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar ‘yan acaba ‘yan Arewa a Jihar Ogun.

Aminiya ta tuntubi Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun a kan lamarin, sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Omotola Odutola ba ta amsa waya ba, ba ta kuma amsa sakon da aka aike mata ba.

Da aka tuntubi Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun ta waya, CP Alamutu ya nemi wakilinmu ya sake kiran sa saboda yana wajen wani taro.