✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu sana’ar alewa sun koka kan tsadar sukari a Kaduna

Malam Abdullahi Aliyu mai haɗa alewa ne da ya kwashe shekara 40 yana sana’ar a Unguwar Tudun Wada.

Masu sana’ar alewa a Kaduna, sun koka a kan matsalar gurguncewar tattallin arzaki da kuma tashin farashin sukari wanda ake amfani da shi wurin yin alewa.

A cewarsu a yanzu buhun sukari ya haura Naira 70,000, kuma ya haifar da kalubale ga masu sana’ar alewa kuma yin shi ba ya kawo riba.

Akasarin masu sana’ar sun nuna buƙatar samun tallafin gwamnati domin su samu ci gaba da harkar.

Ana haɗa alewa ne da sukari da jinja da lemun tsami da ruwa da sauransu.

Malam Abdullahi Aliyu mai haɗa alewa ne da ya kwashe shekara 40 yana sana’ar a Unguwar Tudun Wada, ya bayyana cewa akwai wani  lokacin da yake yin buhu goma a rana saboda kasuwancin alewar na ja.

Amma a yanzu ya ce da kyar yake yin rabin buhu saboda tsadar sukari.

Ya jaddada tasirin haka a kan halin da ake ciki na tattalin arzaki wanda hakan ya tilasta wa da yawa daga abokan sana’arsu canza sana’a.

A cewarsa, “A baya ana sayar da buhun sukari ne Naira 6,000, a yanzu da muke magana, yawanci mutane duk sun bar hakokin kasuwancinsu saboda komai ya yi tsada,” inji shi.

Duk da kalubalen da ake fuskanta, Malam Abdullahi ya bayyana cewa bai tava samun wani ba shi ko tallafin kuɗi ba daga gwamnati ba duk kuwa da ya horar da mutane da yawa a wannan sana’a.

Wani mazaunin Unguwar Badarawa da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Salisu Suleiman ya bayyana cewa ana samun ƙarancin alewa saboda tsadar sukari.

A cewarsa, “Ni da yara na mun fi son mai yaji-yaji. Amma yanzu ba na ganin masu tallar alewa sosai saboda na ji cewa waɗanda suke yi a yanzu sun daina sakamako karuwar farashin sukari.”

Malam Aliyu Zaria mazaunin Unguwar Rigasa ya ce shi ma ya lura masu sayar da alawa sun yi ƙaranci sosai a unguwarsu, kamar shi ma Adamu Hassan ya karfafa bayanin.

Wani tsohon mai sayar da alewa mai suna Malam Abdulmumini Babangida ya ce, “babban dalilin da ya sa sana’ar ba ta bunkasa shi ne tsadar kuɗin sukari, amma akwai wasu mutanen da suke yi a wasu wuraren duk da matsin tattalin arzaki da ake fama da shi a kasar nan.”