A farkon makon jiya ne aka samu labarin cewa, an kama tare da tsare fitaccen darakta a Masana’antar Kannywood, Sanusi Oscar 442.
Wata majiya a Gwamnatin Kano da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, an kama Oscar ne ranar Lahadin makon jiya.
Majiyar ta ce an kama shi ne saboda wani sakon murya da ake zargin ya aika wa wani babba daga cikin jiga-jigan Gwamnatin Kano, inda yake zargin maganar na barazana ga rayuwarsa.
Ta hannun damar Oscar 442, Amina Amisco ce ta ankarar da mutane kamun, inda ta rubuta a shafinta na Facebook cewa, “Tabbas kai dan Kwankwasiyya ne kuma ka jure daka da sassakar makiya Oscar, wanda duk ya san ka ya san ka a gidan Kwankwaso.
“Sai dai kash! duk da wannan gwagwarmayar da ka sha bai hana a ci mutuncinka a wajensu ba. Wai dama haka siyasarku take ta Kano?
“Wane irin rikici ne da har gwamna ba zai iya kashe shi ba sai an kai Abuja. Wannan lamarin akwai abun dubawa gaskiya.
“Wallahi Abun kunya yake ba ni a ce wai ’yan Gandujiyya ba su kama Oscar ba sai ’yan Kwankwasiyya. S.A ya kama SSA Allah Ya kyauta. Za mu yi kokari in sha Allah komai zai wuce, Allah Ya kiyaye gaba.”
Ta sake wani rubutun, inda ta ce, “Wannan ita ce take nuna mana ka yi nasara a rayuwarka darakta. Duk wannan taron dangin kai ɗaya tilo, Innalillahi wa inna ilaihirraji’un.
“Darakta mutumin kirki dan gwagwarmaya wanda kullum ake fada da shi a kan fadin gaskiya.”
Bayan ya fito, a ranar Talata Sanusi Oscar ya rubuta cewa, “Ina so in yi amfani da wannan dama wajen godiya mai tarin yawa ga Mai Girma Gwamna, Allah Ya sa ka gama lafiya, ina kuma ba ka tabbacin muna tare da kai ko wahala ko dadi in sha Allah.
“Bayan dawowa ta a jiya, mun yi doguwar magana da dan uwana Tijjani Gandu, har sai da na zubar da hawaye a kan abubuwan da ya fada min a lokacin ganawarsu da Mai girma Gwamna da suka yi a kaina bisa abin da ya faru da ni.
“Na ji dadi sosai da nuna kulawarsa a kaina.”
Sai dai rubutun da Amisco ta yi tun a farko ya sa aka fara tunanin ko shi da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha ne, kasancewar an san akwai dan taku-saka a tsakaninsu, kafin wata majiyar ta bayyana wa Aminiya cewa, wani jami’in gwamnatin ne daban.
Aminiya ta ruwaito cewa, Kannywood ta kasu kashi hudu ne a siyasa kafin zabe, inda akwai 13×13 karkashin mawaki Dauda Kahutu Rarara da YBN karkashin Abdul Amart Maikwashewa da tsagin Kwankwansiyya, wanda ya kunshi Abba El-Mustapha da Sani Danja da Alhaji Sheshe da sauransu, sai kuma ’yan PDP.
Bayan an yi zaben, za a iya cewa ba a taba samun lokacin da Kannywood ta samu mukamai kamar wannan ba.
A Jihar Kano, an nada Sanusi Oscar 442 mai ba wa gwamna shawara na musamman a kan harkokin Kannywood.
Sai kuma mawaki Tijjani Hussaini Gandu a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin mawaka da mawallafa.
Sai tsohuwar jaruma, Maryam Abubakar Jankunne a matsayin babbar mai ba shi shawara a bangaren matan karkara, bayan kuma nada Abba El-Mustapha, a matsayin Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dabi’i ta Jihar Kano da aka yi.
Haka kuma a Jihar Filato, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ya nada Bashir Lawandi Datti a matsayin Kwamishinan Matasa da Wasanni.
Uwa-uba, an naɗa Ali Nuhu a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Finafinai ta Nijeriya baki daya.
Tun a lokacin ne a wata tattaunawa da Aminiya, Sanusi Oscar 442 ya bayyana cewa, shi ba zai amince da ’yan shan kai ba, wato wadanda ba tare da su aka yi wahala ba, amma suka hauro a sharbi romo da su.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar da aka raka Abba El-Mustapha ofis, ta duba hotunan da aka ta yadawa, amma ba ta hango darakta Sanusi Oscar ba a wajen duk da cewa ba ta da tabbacin ko ya je ko bai je ba.
Tun lokacin ake taku-saka, inda Oscar yake zargin cewa, Abba ya jawo ’yan adawa a jiki, wanda har a lokacin aka jiyo darakta Sheikh Isa Alolo da Alhaji Sheshe suna mayar da martani masu zafi.
Aminiya ta ruwaito tun a 2015 lokacin da jaruman masana’antar suka rabe biyu, tsakanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, kowane bangare ya bayyana cewa, sun shiga siyasar ce domin su jawo wa masana’antar alheri da gyara.
Ana tunanin kasancewar Kannywood ta samu mukamai, za su hada kansu wajen ciyar da masana’antar gaba.
Amma Aminiya ta lura kullum siyasa kara farraka masana’antar take yi, inda yanzu nasarar NNPP ta sa tsagin Kwankwasiyya suka rabe biyu yanzu.
Wasu na tare da Abba El-Mustapha, wasu kuma na tare da Sanusi Oscar 442.
A wani bangaren kuma, Mustapha Naburaska, wanda tsohon dan APC ne, amma ya dawo Kwankwasiyya, ana yawan jiyo yana gugar zana da zage-zage ga wani mawaki da yake alakanta da bako a Kano wanda yake cin mutuncin iyayen gidansu.
A bangaren Rarara ma, an daina ganin sa da manyan na hannun damansa irin su Abubakar Bashir Maishadda da sauransu.
Dama can duk da cewa Abdul Amart da Rarara APCn suke wa aiki, amma ba sa ga-maciji, kuma har yanzu akwai alamar ba a samu sulhu ba.