✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta rufe shagunan magani 1321 a Kano

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC reshen Jihar Kano tare da hadin gwiwar Hukumar da ke Kula da Magunguna…

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC reshen Jihar Kano tare da hadin gwiwar Hukumar da ke Kula da Magunguna ta Kasa sun rufe shagunan magani 1321 da ke Malam Kato da Mai Kari Plaza da kuma cikin Kasuwar Sabon Gari a jihar.

Shugaban Hukumar a Jihar Kano, Kashm Ibrahim ya ce, sun rufe shagunan ne don ganin masu maganin sun bi doka ta hanyar komawa Kasuwar Dangwauro wacce Gwamnatin Jihar ta tanadar musu.

Haka kuma, Kashin Ibrahim ya ce za a ci gaba da samar da wasu shagunan a cikin kasuwar don magance matsalar da ‘yan maganin ke dogaro da ita cewa rashin isassun shagunan ne ya hana su komawa kasuwar.

A cewarsa, magani abu ne da ya shafi rayuwar mutane don haka ba za a dauke shi da wasa ba.

Sai dai masu maganin ta hanyar kungiyarsu ta NAPPMED sun bayyana cewa suma sun rufe shagunansu tare da shiga yajin aikin sayar da magani har sai baba ta gani.

Shugaban Kungiyar Alhaji Muhammad Musbahu Khalid ya bayyana cewa, sun rufe shagunansu ne don gwamnati ta san amfaninsu a Jihar Kano.

Ya kuma musanta batun da ake yi cewa ‘yan kabilar Ibo ne masu sana’ar magani a Kano, “wannan zance ne mara tushe kuma zalinci ne. Muna so al’ummar jihar manya da kanana su sani an yi haka ne saboda zalunci.”

A cewarsa, sabon wurin da ake so a koma na Dangwauro ba na gwamnati ba ne, kawai na wasu ne domin tsawwala wa ’yan kasuwar magani.

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar da ta gabata ce Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano karkashin jagorancin Mai sharia Simon Amobeda ta umarci manyan dilolin masu maganin da su koma Kasuwar Dangwauro don ci gaba da kasuwancinsu.

Hukuncin kotun shi ya kawo karshen takaddamar da aka dauki tsawon shekara biyar ana yi tsakanin bangarorin biyu na hukumar da ke kula da magunguna ta kasa da kuma kungiyar ’yan maganin.