✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matasa ke tafka asara a harkar ‘Crypto’

Bayanin hanyar cin riba da abin da ke jawo asara a harkar crypto ga matasa a Arewacin Najeriya

Harkar kudaden intanet, wato cryptocurrency, harka ce da matasa suka runguma hannu bibbiyu a ’yan wadannan shekarun, inda suke zuba kudade da zummar samun riba cikin kankanin lokaci kuma cikin sauki.

An kirkiro fasahar ‘cryptocurrency’ wadda ake takaita wa da ‘crypto’ ne a lokacin da aka fara samun matsin tattalin arzikin duniya a shekarar 2008.

Satoshi Nakomoto wanda har yanzu ba a da tabbacin wane ne, shi ne ya fara kirkiro kudin intanet, wato ‘Bitcoin’, a karkashin fasahar blockchain, wanda tsari ne da ke bai wa jama’a damar yin mua’amalar kudi ta intanet.

A halin yanzu akwai irin wadanann kudade sama da 200 a kasuwar crypto ta duniya.

Kasuwancin bitcoin ya fara shahara a Najeriya ne a shekarar 2016, lokacin da aka fara samun matsin tattalin arziki a kasar.

Sai dai wahalar sha’anin harkar crypto ta sa da yawa daga ’yan Najeriya sun fi mai da hankali kan zuba hannun jari a harkar maimakon kasuwancin sa a fadin duniya.

Kamfanonin dillacin wannan kudi na yanar gizo wadanda ake kira da ‘exchangers’ wadanda dole sai da su za a samu damar saye da sayarwar wannan crypto sun bulla ne bayan da harkar ta samu karbuwa a hannun al’umma a fadin duniya.

Yadda ake kasuwancin Crypto

Akan sayi wani abu da ake kira da ‘coins’ kamar Bitcoin, Ethereum, Binace Coins, Tether, Codarno, Solana TRON, Algorand da sauransu.

Idan mutum na da ishasshen kudin da zai saya, idan kuma babu to akwai abin da ake kira ‘alternative coins’ ko  ‘tokens’ wadanda suke a karkashin wadannan manyan coins din kuma ake dillancin su a karkashin wadannan kafofi kai tsaye a intanet, sai a  ajiye su, sannan kuma a yi jira zuwa lokacin da za su yi daraja, farashinsu ya tashi a kasuwar.

Har ila yau akwai wasu coins din da ake kira ‘shitcoins’ wadanda ba su da wata daraja a kasuwar sannan  ba su shahara kwarai a kasuwar crypton ba, amma ana sa ran bayan dan lokaci za su sanu a kasuwar kuma su yi daraja.

Irin wadannan a lokacin da suka fito kasuwa ba su da wata daraja, sai dai in an yi sa’a sun karbu a kasuwar sukan ba da riba mai yawa.

Idan kuma aka samu akasin haka shi ke nan an yi asara. A wasu lokacin ma sukan bata a rasa hada-hadarsu shi ke nan an yi asarar duk kudin.

Sai dai masana tattalin arziki na ganin hadahadar crypto barazana ce ga hadahadar kudi a fadin duniya. Wannan ya sa kasashe suka hana harkar su a bankuna.

Sau tari ’yan damfara sukan yi kutse cikin wadannan manhajojin cinikayyar kudi su damfari mutane, sannan kuma ba su da wata takamammiyar hanyar da za a bi diddigi.

Babban Bankin Najeria ma ya hana hadarhadar kudaden crypto.

Duk wadannan coins din da muka ambata darajarsu takan karye ko ta tashi, lamarin ke kawo asara ko riba ga duk wanda yake da su a ajiye.

Abin da ke kawo faduwar kaya ko tashinsu kuma shi ne hasashen da wadanda suka kirkire su da dillalai a harkar suka yi a kan coins din.

Yadda matasan Arewa ke tafka asara

Matasan Arewacin Najeriya da dama kan sanya kudadensu a wannan harka.

Amma akan samu akasi har kudaden nasu su narke saboda rashin sanin kan harkar ko kuma rashin samun wani jagora da da zai bayyana musu yanayin da kasuwa ke ciki.

A wani lokaci kuma asara takan samo asali ne daga karyewar darajar kayan.

Wasu kuma da harkar ta karbe su, kamar Muttaka Salisu Haruna wanda aka fi sani da MK mazaunin Kano ya bayyana cewa rashin bincike a kan harkar da gaggawa ke sa yawancin matasan yin asara.

A cewarsa, “Rashin sanin kasuwanci din kansa shi ya sa suke faduwa, da dama sukan dauka cewa harkar crypto kamar harka ce ta sa biyar ka ci goma.

“Kawai daga mutum ya samu labarin wani abokinsa ya samu riba a harkar kawai shi ma sai ya je ya narka kudi ba tare da sanin takameman yadda harkar take ba.”

‘Na yi nadamar sanya kudina a harkar crypto’

Aminiya ta tattauna da wasu matasa da suka taba harkar, sun kuma bayyana mata yadda suka yi asarar kudin su gaba daya.

Wani matsahi a garin Kano Mustapha Abubakar ya bayyana yadda ya sanya kudinsa a harkar kuma suka narke.

Ya bayyana nadamarsa kan sanya kudinsa har kusan Naira 150,000, wadanda ya yi asarar su babu gaira babu dalili.

“Ni babu wani dalili da zai sa na kara sanya kudina a harkar crypto a halin yanzu, sai dai idan na samu wani kudi da ba abin da zan yi da shi kuma na tabbatar da cewa farashin coins din da zan saya ya karye, sannan kuma yana hawa zan siyar da shi,” a cewar Mustapha.

‘Asarar da na tafka ta sa na daina harkar’

Ibrahim Hussaini wanda aka fi sani da Yaro, mazaunin unguwar Gandun Sarki a garin Hadejia a jihar Jigawa ya shaida cewa yadda ya tafka asarar dubu dari da hamsin ba zai kara sanya kudinsa ba.

Ya ce baya ga rashin tabbas a harkar da ke karya mutane, manyan masu harkar kan karya kanana da gangan, su boye muhimman bayanan da ya kamata su bayyana ga kowane mai harkar, sai a junansu, alhali bayanan ne ke bai wa mutum damar cin riba a kasuwar.

Ya kara da cewa “Duk wanda zai bugi kirji ya ce ya samu wata ribar a zo a gani a harkar crypton nan to tabbas akwai wani babban dillali da yake siyan bayanan sirri daga gare shi.

“Su wadannan manyan su ke zama su tsara irin yadda kaya za su tashi ko su karye, kuma suna shiryawa ne da wadanda suka kirkiro coins din wajen karyawa ko tayar da kowane irin coins”.

‘Babu ruwa na da wannan cacar’

Yunus Ibrahim mazaunin garin Maiduguri a Jihar Borno ya ce harkar crypto tamkar caca ce, babu wani dalili da zai sa ya sake zuba kudinsa.

Ya ce shi da Allah Ya rufa masa asiri bayan rushewar kudin nasa a karon farko ya samu nasarar fanshewa a hankali, amma fa da kyar, kuma ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya samu nasarar dawo da kudin gaba daya.

Sannan ya ce ko wani dan uwansa ya gani yana kokarin shiga harkar zai yi kokarin nusar da shi irin hadarin da ke ciki.