✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matan da aka saki ke yin biki na musamman a Mauritaniya

Dangi da ƙawaye kan kewaye matar da aka saki, suna murna da sabon ’yancin da ta samu.

A ƙasar Mauritaniya, sakin aure ba rabuwar aure ba ne da ake ki, idan ya faru ana yin shagulgula musamman a tsakanin mata, a matsayin wata alama ta samun sabon ’yanci da dama.

Wannan lamari na al’ada da ke nuna karfin ikon mace n a kabilar Moorish a kasar, inda mata ke jin dadin samun damar cin gashin kansu da kuma karfafa masu sake yin aure.

Duk da damuwa game da kwanciyar hankali na iyali da abubuwan da suka shafi tattalin arziki, kasuwar saki tana ba mata dama da sake fasalin al’adar.

Ga yawancin matan Mauritaniya, sakin aure na nufin bikin fara sabuwar rayuwa da makoma ta gaba mai gamsarwa.

Kasar Mauritaniya, kasa ce da ke cikin hamada, tana da wani al’amari na musamman na al’adu da suka sha bamban da ka’idojin da suka shafi sakin aure a duniya.

A wannan kasa da ke Arewa maso Yammacin Afirka, sakin aure ba kawai ya zama ruwan dare ba ne, har ma ana shirya shagulgula ga matan, waɗanda galibi ke samun kansu a tsakiyar bukukuwan da ake yi na kawo ƙarshen aurensu.

Manufar ‘kasuwar saki’ a Mauritaniya ba kasuwa ce yadda aka sani ba ta al’ada, a’a, aba ce da matan da aka saki su za su iya sake kafa matsayinsu na zamantakewa kuma ana ganin suna da sha’awar sake yin aure.

Wannan dai wani lamari ne da ke nuni da al’adun kabilar Moorish na kasar, da a tarihi ke bai wa mata damar cin gashin kai da ’yanci, musamman idan aka kwatanta da sauran kasashen Larabawa.

A ƙasar Mauritaniya, ba kasafai ake samun rabuwar aure ba, inda wasu alkaluma ke nuna cewa kusan kashi uku na ma’auratan na wargajewa.

Duk da haka, ba kamar al’adu da yawa da sakin aure ke haifar da tsangwama ba, a Mauritaniya, sau da yawa yakan zama dalilin yin biki.

Dangi da ƙawaye kan kewaye matar da aka saki, suna murna da sabon ’yancin da ta samu ta hanyar kade-kade, raye-raye da liyafa.

Waɗannan tarurruka ba taron jama’a ba ne kawai, har ma da bayyana ra’ayoyin jama’a na kasancewar mace don ta sake yin aure.

Sakin aure a Mauritaniya na haifar da abin da wasu masana ilimin zamantakewa ke kira da ‘dama ce ta yin wani aure,’ inda mata za su iya yin aure sau da yawa a rayuwarsu.

Ana ganin macen da ta samu kwarewa daga zaman auren da ta yi a baya za ta iya samun kyakkyawan matsayi fiye da budurwa, wadda ba ta da ƙwarewar zaman aure.

Wannan hangen nesa yana ba mata damar fara neman saki idan sun ji ba a biya musu bukatunsu, suna kalubalantar labarin gargajiya na mata masu shiga tsakani a cikin aure.

Shari’ar Musulunci da ta tsara aure da saki a kasar Mauritaniya, ta hada da wani tanadi da aka fi sani da ‘khul’i’, wanda ke bai wa mace damar neman saki ta hanyar biyan diyya ga mijinta, yawanci ta hanyar mayar da sadakin matar.

Wannan tsarin ya bai wa mata wata dama a hukumance wajen kawo karshen aurensu, abin da ba kasafai ake samu ba a kasashen Musulmi da dama.

Bikin saki a Mauritaniya na nuna irin tsarin da kasar ke da shi na musamman game da auratayya da yanayin jinsi.

Al’umma ce da kimar mace ba ta raguwa saboda saki; maimakon haka, sau da yawa tana karuwa.

Ana kallon matan da aka sake su a matsayin masu gwaninta kuma masu hikima, sun samu fahimta da kwarewa daga abubuwan da suka faru a baya na zaman aure.