Wani saurayi ya wallafa wani labarinsa a kafar sada zumunta ta Reddit tare da yin nadama, inda ya ce matar da suke soyayya ta faɗa masa cewa, an haife ta ne a shekarar 1998, har sai da ya duba bayanan fasfo dinta.
A wani lamari mai ban al’ajabi da ban tsoro, matashin ɗan shekara 26 ya girgiza bayan ya gano cewa, matar da yake soyayya da ita da nufin aure, bayan shafe shekaru huɗu suna tare tana da shekara 47, ba 27 ba, kamar yadda ta yi iƙirari.
Saurayin ya tafi shafin Reddit don ya wallafa labarinsa na nadama, inda ya ce, matar ta sha gaya masa cewa, an haife ta ne a watan Afrilun 1998, amma ya gano an haife ta a 1977 shekara 48 ke nan.
Saurayin ya rubuta a cikin shafin intanet cewa, “ina soyayya tare da budurwata har tsawon shekaru 4, kuma koyaushe tana ikirarin an haife ta a watan Afrilu ‘1998, amma na gano a ainihin lokacin da aka haife ta shi ne 1977.
Saurayin ya ce, ba shi da wani dalili na yin shakku, domin matar ta yi kama da ’yar shekara 27, ba wanda ya taba tunanin ta kusa 50 ba, amma ya yarda cewa akwai wasu alamomi a tsawon tafiyar soyayyar.
“Akwai wasu alamomi a lokacin da muke tare, amma na zabi in yi watsi da su tunda ba ni da gogewa kan gano ainihin (wannan ita ce alakar soyayya ta ta farko mai tsawo),” in ji shi, inda ya kara da cewa, matar ta damu da kamanninta, kuma duk kawayenta sun fi shekara 27 sosai.
“Duk lokacin da na nemi ta nuna min wasu takardu kamar fasfo sai ta ƙi nuna min, ta ba da uzuri na banza da kokarin kauce wa batun.”
A yayin binciken, saurayin ya kuma sami hoton gwajin ciki, wanda ’yan watanni kafin su hadu kuma su fara soyayya.
Kafofin sada zumunta na zamani sun mayar da martani kan batun, yayin da sakonni suka yi ta yaduwa, daruruwan mutane sun sharhi, inda akasari ke fada wa mutumin ya kawo karshen dangantakarsa da matar da aka gina ta bisa karya.