✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mata ta kusa tsinke mazakutar mijinta saboda kishi

Wata mata da ake zargi da yi wa mijinta lahani a mazakutarta na fuskantar bincike a hannun Rundunar Tsaron Farar Hula (NSCDC) a jihar Osun.…

Wata mata da ake zargi da yi wa mijinta lahani a mazakutarta na fuskantar bincike a hannun Rundunar Tsaron Farar Hula (NSCDC) a jihar Osun.

Rundunar ta samu mijin matar cikin mawuyacin halin rashin lafiya da ciwon jiki sakamakon illar ta matar tasa yi masa a marainansa.

Kakakin NCDC a jihar Osun Daniel Adigun ya ce da farko matar wadda ke zaune a yankin Ikiru ta Karamar Hukumar Ifelodun ce ta kai wa rundunar kara cewa mijin nata ba ya sauke hakkin da ke kansa na aure.

Ko da suka gayyace shi, sai suka same shi cikin mawuyacin hali sakamakon murde marainansa da ta yi tana neman tsinke su saboda sabanin da suka samu, lamarin da ya sa ita ma suka fara yi mata tambayoyi.

Ya ce shekarun ma’auratan shida da yin aure har da ‘yaya biyu, amma “Mijin ya yi korafin cewa bai taba jin dadin auren ba, domin matar kan kama shi da fada a kowane lokaci, lamarin da ya sanya shi yin kaura ya koma unguwar Iragbiji da zama.

“Yana a zaune nan ne wata rana da misalin karfe 10 na dare wata mata ta kawo masa abinci amma ruwa ya tsare ta sai ta jira a dakinsa kafin ruwan ya dauke.

“Bai yi aune ba sai ya ji an kwankwasa kofa, da ya bude sai ya tarar matarshi ce, ita kuma nan take ta haushi da fada, saboda matar da ta gani, ta kama ‘ya’yan marainansa ta murde su tana kokarin tsinka su.

“Ya ce daga nan bai kara sanin inda kan shi yake ba, sai farkawa ya yi ya gan shi a gadon asibiti inda aka yi masa aiki a raunin da ta yi masa a marainan nasa” inji shi.

Jami’in ya kara da cewa matar mutumin ta shaida musu ce ta yi masa haka ne a kokarinta na kare kanta a lokacin saboda ya yi yunkurin far mata.

Ta ce ta bi sawun mijin nata ne saboda tana zargin yana hulda da wata mata bayan ya bar gidanta, kuma kwatsam sai ta iske shi tare da matar.