Maza a yankunan Arewa suna barin garuruwansu zuwa wasu jihohi domin ci-rani a kokarinsu na neman abin sakawa a bakin salati musamman saboda kuncin tattalin arziki da rashin aikin yi da rashin tsaro da rashin kudi da akan yi fama da su a yankunan nasu.
Binciken Aminiya ya gano cewa hana acaba a garin Minna a Jihar Neja na cikin abubuwan da suka sa irin wadannan magidanta musamman matasa yin kaura zuwa jihohin Kogi da Legas da kuma garin Zuba da ke Abuja domin neman abin yi.
- An kashe jami’an Civil Defence 7 a Jihar Neja
- Daga Laraba: Yadda kuri’arku za ta iya sauya rayuwarku
Aminiya ta kuma gano tafiya ci-ranin da maza ke yi ya taimaka wajen kara dora wa matansu nauyin kula da ’ya’yansu da kuma gida wanda haka ke tilasta wa wadansu matan neman a sake su saboda wahalar da suke sha da kuma dadewa da wadansu mazan suke yi idan sun tafi.
‘Babu dadi rashin kasancewa mazanmu a kusa da mu’
Daya daga cikin matan da suke fuskantar irin wannan matsala wadda ba ta so a ambaci sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, “Babu abin da ke damuna kamar dadewar da mijina ke yi idan ya tafi ci-rani.
“Akwai lokacin da dana ya yi rashin lafiya kuma rashin lafiyar a cikin dare ya zo masa misalin karfe 12:00 na dare. Ban san yadda zan yi ba duk na rikice sannan ga mijina yana Kaduna.
“Makwabcinmu ne ya taimaka min ya dauke mu a kan babur zuwa asibiti.”
Wata matar aure da mijinta ke aiki a Abuja a matsayin direban tasi cewa ta yi, “Gaskiya abin babu dadi ka kasance nesa da mijinka musamman ’ya’yanka.
“Yaran sukan ji kewar mahaifinsu.
“Ina zaune ne a gidan da kowace mata take tare da mijinta.
“Wani lokaci idan ’yata ta ga sauran yara tare da iyayansu maza sai ta rika tambayata ina mahaifinta,” inji ta.
Wata mai shekara 43, Misis Luisy Sunday ’yar asalin Jihar Benuwai da ke zaune a Lafiya a Jihar Nasarawa cewa ta yi ta fara sayar da kunun dawa ne domin kare mutuncinta duk da cewa mijinta yana aiko mata da Naira dubu 15 a duk wata.
“Wasu lokuta ba ya zuwa duba mu a Lafiya saboda yanayin aikinsa. Kuma lokacin da ya zo duba mu yakan kasance cikin damuwa saboda yana duba yadda zai kare kansa daga talauci,” inji ta.
‘Nema muke zuwa’
Malam Lawali wanda ya bar iyalansa a Jihar Kebbi ya bude shagon kayan masarufi a garin Minna ya ce sau daya yake ziyartar matansa biyu da suke Kebbi a shekara, kuma sai a watan azumi.
“Sun yi korafi har sun hakura tunda dai fita nake in je in nemo abin da zan kula da su. Ina kiran su a waya kullum kuma so suke in rika ziyartarsu a-kai-a -kai amma abu ne mai wuya,” inji shi.
“Shi ma wani magidanci Mohammed wanda a yanzu yake Jihar Kano yana ci-rani ya ce matarsa ta yi masa barazanar neman saki idan har ba zai nemi wata sana’a da zai rika yi a gida ba.
“Koda yake daga bisani ta fahimci halin da ake ciki wanda hakan ya sa ina komawa gida a -kai-a-kai,” inji shi.
Shi ma Abubakar Mohammed Galbu mutumin Karamar Hukumar Bindawa a Jihar Katsina wanda yake sana’a a Jihar Kaduna ya bar matarsa da ’ya’yansa ne a kauyensu.
Sai dai ya ce ba ya wuce kwana 40 bai koma gida ba domin ganin iyalansa.
A cewarsa ko addini da ma kwana 40 ya ba wa maza damar barin iyalinsu.
Da yake bayyana dalilan da suke sa maza barin garuruwansu zuwa ci-rani, ya ce akwai talauci da rashin aikin yi da bashi da kuma sabanin dangi.
Sai dai a cewarsa a yanzu zuwan wayar hannu ta taimaka matuka tunda mazan kan kira gida domin yin magana da iyalansu a-kai-a-kai.
“Ba na wuce kwana 40 ban je kauye ba. Koda yake akwai wadansu mazan da suke barin garuruwansu tun suna matasa kuma har su manyanta ba za su koma gida ba.
“Wadansu har su yi aure a bariki su bar matansu na farko a kauye,” inji shi.
Ya kara da cewa wasu lokutan mata kan bukaci a raba aurensu da mazan da suka bar garinsu na tsawon shekaru ba su koma ba.
‘Abin da ya sa wadansu ke dadewa ba su koma ba’
Shi kuwa Musa Dallaji ya ce duk wata yake komawa gida Katsina wajen iyalansa, inda ya ce akasarin mazan da suka bar kauyukansu da nufin zuwa nema suna kin komawa garinsu ne saboda kunyar rashin samun dukiyar da suka fita nema.
“Akasarinsu suna zaune a Legas da Fatakwal da kuma wasu jihohin Kudu.
“Amma ni a kauyanmu akwai maza da yawa da suka fita nema kuma yawancinsu suna tabbatar da sun koma gida wurin iyalansu bayan ’yan wasu lokuta, domin ganin ’ya’yansu da sauran ’yan uwa,” inji shi.
Dole magidanta su nemi hanyoyin kasancewa da iyalansu —Malamin Jami’a
Da yake bayani a kan tabarbarewar tattalin arzikin magidanta wanda ke tilasta tafiya ci-rani saboda samun damar kula da iyalansu, wani masani kuma malami a Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa, Dokta Jacob Pristine Magip ya ce yanayin babu dadi.
Ya shawarci ma’aurata su rika tunanin wasu hanyoyin neman halaliyarsu ba tare da sai sun bar garuruwan da suke da iyalansu ba.
Ya ce ma’aurata suna bukatar kasancewa wuri guda ne domin faranta wa juna rai.
Ya ce “Sai dai akwai karuwar rashin aikin yi a ko’ina wannan ya sa idan miji ko mata suka samu aiki a wata jiha ba na tsammanin daya daga cikinsu zai yi watsi da aikin saboda kawai suna son zama tare.”
Ya kara da cewa yawancin tsare-tsaren gwamnati ciki har da karin kudin wutar lantarki da rashin daidaito a kan farashin man fetur ne suka janyo rushewar zamantakewar iyalai da yawa a wannan kasa.