✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ma’aikacin KEDCO ya kashe abokin aikinsa a Kano

Wanda ake zargin ya shaida wa ’yan sanda cewa marigayin ya karɓi kuɗi a hannunsa har N3m.

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu, bisa zargin kisan abokinsa Bello Bukar Adam wanda ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jihar Kano (KEDCO) ne.

Sadiq Zubairu mai shekaru 35 da ke zaune a unguwar Hotoron Nasarawa ya shaida wa ’yan sanda yadda ya shi da wasu da a yanzu aka baza komar kama su suka yaudari abokin aikin nasa, suka lakada masa dukan da ya yi ajalinsa.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

SP Kiyawa ya ce a ranar 5 ga watan Mayu ne rundunar ’yan sanda ta samu ƙorafin ɓatan Bello Bukar Adam mai shekara 45, wanda aka ce ya bar gida tun ranar 4 ga watan Mayun.

Sanarwar ta ce a yammacin wannan ranar ce kuma ’yan sanda suka samu rahoton tsintar gawar mutumin, wanda aka jefar a ƙauyen Bechi da ke yankin Karamar Hukumar Kumbotso.

Ya ce nan take rundunar ’yan sanda ta tura tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin DPO na ƙaramar hukumar, SP Mustafa Abubakar, inda suka ɗauko gawar zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, wanda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

A nan take rundunar ’yan sanda ta ƙaddamar da bincike tare da kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu mai shekara 35 da ke unguwar Hotoron Arewa bisa zargin aikata laifin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a lokacin da ’yan sandar ke tuhumar wanda ake zargin, ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutum biyu wajen fito da Bello — wanda ya kasance abokinsa ne — daga gidansa.

Sadiq ya shaida wa ’yan sanda cewa da kansa ya ɗaure Bello inda suka rika dukansa da sanduna da ƙarafa masu kaifi a kansa da sauran sassan jikinsa har sai da ya mutu.

“Bayan ya mutu ne suka sanya shi jikin but ɗin motarsa, tare da jefar da gawar a kan titin Eastern Bypass, a daidai ƙauyen Bechi, inda suka gudu da motar, ƙirar Toyota Corolla 2015, da kuma wayar marigayin”, kamar yadda sanarwar ’yan sandan ta yi bayani

“Haka kuma wanda ake zargin ya shaida wa ’yan sandan cewa dalilinsu na aikata hakan shi ne marigayin ya karɓi kuɗi har naira miliyan uku daga wajensa da nufin zai sama masa aiki.

“Amma sai daga baya ya fahimci cewa marigayin ba zai sama masa aikin ba, kan hakan ne ya haɗa baki da wasu mutum biyu domin kashe shi tare da yin awon gaba da motarsa inda suka ɓoye ta a wani gareji da ke unguwar Hotoro.”

Kiyawa ya ce kara da cewa, an samu nasarar cafke Sadiq Zubairu cikin gaggawa bayan Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel ya tura tawagar yaki da masu garkuwa da mutane karkashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal da aka bai wa umarnin cika aikin cikin sa’o’i 24.

CP Gumel wanda ya bayyana takaicinsa dangane da faruwar wannan lamari tare da jajanta wa ’yan uwan marigayin, ya kuma bai wa jama’ar Kano tabbacin cewa za su ci gaba da jajircewa wajen tsaron lafiya da dukiyar al’umma a jihar.