✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Finidi George ya doke Turawa wajen zama Kocin Super Eagles

Waɗanda suka horar da Super Eagles daga farko zuwa yanzu da ƙasashensu.

A ranar Litinin ta makon jiya ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF) ta sanar da nada tsohon dan wasan Super Eagles Finidi George a matsayin sabon kocin babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles.

Kakakin Hukumar NFF, Ademola Olajire ne ya fitar da sanarwar, inda ya ce Finidi ne zai ci gaba da horar da Super Eagles.

Finidi George wanda tsohon dan wasan Super Eagles ne, ya shafe wata 20 a matsayin Mataimakin tsohon kocin kungiyar, José Peseiro, wanda ya jagorance ta suka lashe lambar azurfa a gasar Nahiyar Afirka (AFCON 2023) a Kasar Kwaddibuwa.

Jim kadan da kammala gasar AFCON 2023 Peseiro dan kasar Portugal ya yi murabus don kashin kansa, daga nan Finidi George ya ci gaba da horar da ’yan wasan a matsayin riko.

Ba a yi tsammanin Finidi George zai zama kocin kungiyar ba, kasancewar an fi sa ran tsohon dan wasan Nijeriya, Emmanuel Amuneke, wanda ake ganin ya fi Finidi kwarewa da sanin makamar aiki, sannan akwai wasu Turawa da ake ganin sun nuna sha’awar horar da kungiyar.

A wata biyu da suka gabata George ya jagoranci Super Eagles a wasannin sada zumuta biyu a kasar Maroko, inda a wasan farko ta lallasa Ghana da ci 2-1, wanda ya kawo karshe shekara 18 a jere da Ghana ke doke ta. Sai dai Super Eagles ta sha kashi da ci 2-0 a hannun kasar Mali.

Finidi George na cikin ’yan wasan Nijeriya da suka lashe Gasar AFCON 1994 a kasar Tunisiya.

Su ne kuma suka zama na biyu wajen kayatar da masu kallo a gasar Kofin Duniya a 1994 a kasar Amurka, wanda shi ne karon farko da Nijeriya ta buga gasar.

Sabon kocin na Super Eagles ya ci wa Nijeriya kwallo 63, sannan sau biyu yana zuwa Gasar Kofin Duniya, a 1994 da 1998.

A shekarun 1992, 1994 da 2000 ya samu kambunan zinare, azurfa da tagulla a gasannin AFCON.

Kwallon Finidi George ta farko a Gasar AFCON ita ce wadda ya zura a wasan Nijeriya da Burkina Faso a Babban Filin Wasa na Kasa da ke Legas a 1991.

Shi ne kuma ya taimaka wa marigayi Rashidi Yekini cin kwallon Nijeriya na farko a gasar Kofin Duniya a 1994, a wasansu da kasar Bulgeriya a Amurka.

Sannan shi ne dan wasan da ya zura kwallon da ta kai Nijeriya ga gasar wanda shi ne karon farko da Super Eagles suka shiga Gasar Cin kofin Duniya.

A bangaren wasannin kungiya kuwa, ya fara taka leda ne a kungiyoyin Calabar Robers da Iwuanyanwu Nationale da Sharks FC kafin ya samu damar zuwa Turai.

A Turai, Kungiyar Ajax ya fara taka wa leda, inda ya buga wasa 85 sannan ya zura kwallo 18 a 1993 zuwa 1996, kafin ya koma Kungiyar Real Betis, inda ya buga wasa 130 a kungiar ta Spain, ya zura kwallo 38 a 1996 zuwa shekarar 2000.

A shekarar 2001 ne ya koma Kungiyar Real Mallorca, inda ya buga wasa 31 ya zura kwallo 5 a shekara daya, sannan ya koma Ingila, inda ya yi shekara uku a Kungiyar Ipswich Town, ya buga wasa 35, ya zura kwallo 7, kafin ya dawo Mallorca.

Nasarorin da ya samu

Ya lashe kofuna da dama a rayuwarsa. Ya lashe kofin babbar gasar Holland, wato Eredibisie sau uku a kakar: 1993-1994, 1994-1995, 1995-1996, sannan ya lashe Kofin Johan Cruijff Shield a 1994 da 1995.

Yana cikin ayarin Ajax da suka lashe Gasar Zakarun Turai a kakar 1994-1995, sannan aka doke su a wasan karshe a kakar 1995-1996.

Ya kuma lashe Gasar Gwanaye ta UEFA Super Cup a1995, sannan ya lashe kofin Intercontinental Cup a 1995.

Zama koci

Bayan ya yi ritaya, sai ya koma makarantar koyon zama koci, inda a shekarar 2021 ya fara da horar da Kungiyar Enyimba FC da ke Jihar Abiya, inda yake aiki har aka gai daukarsa a matsayin Mataimakin Pesero.

Wannan matsayin na Finidi ya samu, ana sa ran zai taimaka wajen kara daga darajar Gasar Firimiya ta Nijeriya, kasancewar daga gasar ya zama kocin kasar nan.

Babban aikin da ke gabansa shi ne sama wa Super Eagles gurbi a kasar cin Kofin Duniya na 2026, ta hanyar yin nasara a wasanninta da kasashen Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin nan da kimanin mako biyar masu zuwa.

Wadanda suka horar da Super Eagles daga farko zuwa yanzu da kasashensu

Jack Finch (1949)-Ingila

Daniel Anyiam (1954-1956)- Nijeriya

Les Courtier (1956-1960)- Ingila Moshe “Jerry” Beit haLevi (1960-1961)-Isra’ila

George Vardar (1961-1963)- Hungary

Joey Blackwell (1963-1964)-Ingila

Daniel Anyiam (1964-1965)-Nijeriya József Ember (1965-1968)- Hungary

Sabino Barinaga (1968-1969)- Spain

Peter ‘Eto’ Amaechina (1969-1970)-Nijeriya Karl-Heinz Marotzke (1970- 1971)- West Germany

Jorge Penna (1972-1973)- Brazil

Karl-Heinz Marotzke (1974)- Jamus ta Yamma

Tihomir Jelisaɓčić (1974- 1978)- Yugoslaɓia

Otto Glória (1979-1982)- Brazil Gottlieb Göller (1981)- Jamus ta Yamma

Festus Onigbinde (1983-1984)-Nijeriya Chris Udemezue (1984-1986)-Nijeriya

Patrick Ekeji (1985)- Nijeriya Paul Hamilton (1987-1989)- Nijeriya

Manfred Höner (jr) (1988- 1989)- Jamus ta Yamma Clemens Westerhof (1989- 1994)- Netherlands

Shaibu Amodu (1994-1995)-Nijeriya

Jo Bonfrere (1995-1996)- Netherlands

Shaibu Amodu (1996-1997)-Nijeriya Philippe Troussier (1997)-Faransa

Monday Sinclair (1997-1998)-Nijeriya Bora Milutinoɓić (1998)- Yugoslaɓia

Thijs Libregts (1999)- Netherlands

Jo Bonfrere (1999-2001)- Netherlands

Shaibu Amodu (2001-2002)-Nijeriya

Festus Onigbinde (2002)-Nijeriya

Christian Chukwu (2002-2005)-Nijeriya Augustine Eguaɓoen (2005-2007)-Nijeriya

Berti Ɓogts (2007-2008)- Jamus

James Peters (2008)-Nijeriya Shaibu Amodu (2008-2010)-Nijeriya

Lars Lagerbäck (2010)-Sweden

Augustine Eguaxoen (2010)-Nijeriya

Samson Siasia (2010-2011)- Nijeriya

Stephen Keshi (2011-2014)- Nijeriya

Shaibu Amodu (2014)- Nijeriya

Stephen Keshi (2014)- Nijeriya

Daniel Amokachi (2014- 2015)- Nijeriya

Stephen Keshi (2015)- Nijeriya

Sunday Oliseh (2015-2016) – Nijeriya

Gernot Rohr (2016-2021)- Jamus

Augustine Eguaxoen (2021- 2022) – Nijeriya

Jose Peseiro (2022-2024)- Portugal

Finidi George (2024 )- Nijeriya