Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta naɗa Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles.
Naɗin na Chelle ya samu amincewa bayan taron da NFF ta gudanar a Abuja a ranar 2 ga watan Janairu, 2025, sannan aka kammala amincewa da shi a ranar 7 ga watan Janairu, 2025.
- Abba ya nemi Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin Hajjin 2025
- Zulum ya amince da sauya sunan Jami’ar Borno zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim
Chelle, wanda ke da shekaru 47, tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali, ya jagoranci kulab da dama kamar GS Consolat, FC Martigues, Boulogne, da MC Oran.
A lokacin da yake wasa, Chelle ya buga ƙwallo a kulab ɗin ƙasar Faransa irin su Martigues, Valenciennes, da Lens.
An haifi Chelle a ƙasar Côte d’Ivoire, daga mahaifi ɗan asalin Faransa da mahaifiya ‘yar ƙasar Mali.
Ya zaɓi yin wasa da Mali, inda ya taka leda a wasannin ƙasa guda biyar kafin ya yi ritaya daga wasannin ƙwallo.
Chelle ya jagoranci tawagar Mali daga 2022 zuwa 2024, inda ya kai su zuwa matakin kwata-fayinal a gasar Cin Kofin Afirka ta 2023 (AFCON).
Chelle ya karbi shugabancin Super Eagles bayan Finidi George ya murabus saboda rashin nasara a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.
Aikin Chelle na farko zai zama jagorantar Najeriya zuwa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.