✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu

Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74.

Tsohon ɗan wasa, kuma tsohon mai horas da ’yan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu ya rasu.

Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74.

Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) ta 1980.

Dakta Olusegun Odegbami, tsohon ɗan wasan Najeriya kuma abokin Chukwu, ya tabbatar rasuwar mai ban tausayi a saƙon da ya wallafa ta manhajar sada zumunta X.

“Na samu labarin cewa tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na safiyar yau Asabar, Christian Chukwu, MFR, wanda aka fi sani da Chairman abokina kuma abokin wasana, ɗaya daga cikin manyan ’yan wasan ƙwallon ƙafa a tarihin Najeriya, ya rasu.