✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano

Yajin aikin nasu zai jefa Kano da kewaye cikin duhu.

Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya (NUEE) reshen Jihar Kano, ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani saboda rashin biyan haƙƙoƙinsu da kamfanin KEDCO ke yi.

Sakataren tsare-tsaren ƙungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Muhammad Babangida ne, ya bayyana hakan a wani saƙon murya da Freedom Radio ta wallafa.

A cewarsa, ma’aikatan KEDCO sun shafe sama da watanni 100 ana cire musu kuɗin fansho daga albashinsu, amma ba a tura kuɗin zuwa inda ya dace ba.

“Tun bayan kafa KEDCO aka fara cire wa ma’aikata kuɗin fansho, amma har zuwa yanzu ba a tura su inda ya kamata.

“Waɗanda suka mutu ko suka bar aiki suna cikin wannan hali, ba a biya su haƙƙinsu ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk wani ƙoƙarin da suka yi don sulhu da kamfanin ya ci tura, hakan ya sa suka yanke shawarar shiga yajin aiki.

Ya ce: “Kamfanin KEDCO yana samun kuɗi sosai, amma ya gaza biyan haƙƙin ma’aikata.

“Saboda haka, daga idan mutane sun ga an samu katsewar wuta, ka da su ɗora laifi a kanmu.”

Yajin aikin zai shafi harkokin samar da wutar lantarki a Kano da kewaye.