Jami’an tsaro a kasar Afirka ta Kudu sun shiga bincike kan wani manomi farar fata ya harbe wata bakar fata da ya ce ya dauka dorinar ruwa ce.
Mutumin mai suna Paul Hendrik van Zyl, mai shekara 77, ya shiga hannun jami’an tsaro kasar, bayan da ya dirka wa matar harbi a yayin da take yin su a garin Lephalele.
- Yaki: Amurka za ta tallafa wa Ukraine da Dala biliyan 33
- Tahir Fadlallah: Mai otal din Tahir Guest Palace da ke Kano ya rasu
An tuhumar mutumin da yunkurin kisan kai saboda raunuka matar ta samu, a cewar masu gabatar da kara na kasar.
Sai dai baturen ya musanta kisan matar da gangan, saboda ya dauka dorinar ruwa ce ke neman kai mishi farmaki yayin da ya hango ta daga nesa.
Kakakin ’yan sandan yankin, Mamphasa Seabi, ya ce ana tunanin wanda ake zargin ya harbi matar ne a zaton dorinar ruwa ce a wurin.