Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi zargin tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bullo da sake fasalin Naira ne don kawo cikas ga zaben da ya gabata.
Aminiya ta rawaito yadda Emefiele, a watan Oktoban 2022 ya sanar da matakin bankin na sauya fasalin takardun kudi N200, N500 da kuma N1,000.
- Mun gaji da alkawuran yaudara – ’Yan ƙwadago ga Tinubu
- Za mu tsayar da komai cak a Najeriya ranar 3 ga watan Oktoba – ’Yan kwadago
Daga bisani dai Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin ci gaba da tsofaffin takardun kudin har zuwa ranar 31 ga Janairun 2023.
Sai dai sauya fasalin kudin ya haifar da rudani da shiga tsaka mai wuya a tsakanin ’yan kasar.
Da yake magana a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata, yayin tantance Olayemi Cardoso, a matsayin sabon Gwamnan CBN da mataimakansa hudu, Akapbio ya gargadi Cardoso wajen shiga harkokin siyasa.
Akpabio ya kuma ce tsohon Gwamnan na CBN ya shirya manakisa wajen gurgunta zaben 2023 da ya gabata.
Kazalika ya ce babu kasar da ta taba sauya fasalin kudinta tana shirin shiga babban zabe.
A wancan lokacin da aka sauya fasalin kudin Najeriya, Emefiele ya samu goyon bayan tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.
Hakan ya sanya masu sharhi kan harkokin siyasa da masana tattalin arziki tafka muhawara kan sauya fasalin naira.