✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu tsayar da komai cak a Najeriya ranar 3 ga watan Oktoba – ’Yan kwadago

Kungiyar ta ce za ta tsayar da komai cak a fadin Najeriya

Ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun amince su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a duk fadin Najeriya daga ranar 3 ga watan Oktoba.

Kungiyoyin sun umarci dukkan mambobinsu da rassansu a fadin Najeriya da su tsayar da komai cak a fadin daga ranar Talatar mai zuwa.

Shugabannin kungiyoyin, Joe Ajaero na NLC da Festus Osifo na TUC ne suka bayyana hakan ga manema labarai jim kadan da kammala wani taronsu na gaggawa a sakatariyar ’yan kwadago ta kasa da ke Abuja ranar Talata.

Sun ce za su tsunduma yajin aikin ne saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alkawuran da ta yi musu domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.

’Yan kwadagon sun ce za a ci gaba da yajin aikin ne har sai abin da hali ya yi.

A baya dai ƙungiyoyin sun ba gwamnatin wa’adin kwana 21 domin ta biya musu bukatun, amma wa’adin ya cika a makon da ya gabata ba tare da cim ma wata matsaya ba.

Ko a farkon watan Satumbar nan sai da kungiyoyin suka yi yajin aikin gargadi na kwana biyu, sannan suka ce a shirye suke su wuce ma har sai abin da hali ya yi zuwa karshen watan.

Daga cikin bukatun nasu har da na karin albashi da kuma na rage wasu haraji da ma’aikatan Najeriya ke biya domin su rage radadin.