✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun ba gwamnati kwana 7 ta soke karin kudin lantarki —NLC

Kungiyar kwadago ta ce yin karin kudin lantarki alhali ba a samun wutar yadda ya kamata tamkar yin fashi ne da tsakar rana

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ba wa gwamnati da kamfaninin wutar lantarki wa’adin mako guda s soke karin kudin da suka yi a kasar. 

Shugaban NLC na Kasa, Kwamred Joe Ajaero da takwaransa na Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikata (TUC), Fetus Osifo, ne suka ba da wa’adin a jawabinsu na hadin gwiwa albarkacin zagayowar bikin ranar ma’aikata a Abuja ranar Laraba.

“Rashin adalci ne a tsawalla wa dan Najeriya ya biya kudin wutar da ba samu yake yi ba.

“Kudin wutar lantarki da ake cajin jama’a ya zarce kima, kuma fashi ne rana tsaka ake wa ’yan Najeriya,” in ji shugabannin kwadagon.

Don haka suka ce ya zama dole Hukumar Wutar Lantarki (NERC) da kamfanonin wutar su soke karin kudin wutar.

Kungiyoyin sun bayyana takaicinsu bisa rashin samun tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya, inda suka bayyana cewa hakan yana kawo koma-baya ga cigaban tattalin arzikin kasar.

Sun bayyana cewa duk kasar da ta gaza sama wa kanta wadacciyar wutar lantar lantarki da makamashi, babu makawa sai ta samu koma-baya.

“Babban abin da ke kawo cikas ga ci gaban kasarmu shi ne gazawa wajen gudanar da bangaren lantarki da kulawa da walwalar jama’a.

“Wutar lantarki babban jigo ne wajen farfado da tatalin arziki, kamar yadda bangaren mai da iskar gas ke kan gaba wajen samar da makamashi.”

Sun bayyana cewa don haka ya zama dole gwamnati ta hada hannu da al’ummar kasa wajen samar da tsarin da zai tabbatar da samuwar makamashi mai dorewa ga al’ummar Najeriya.

Shugabannin kwadagon sun jaddada cewa sama da shekara 10 da gwamnati ta cefanar wa ’yan kasuwa bangaren samar da wutar lantarki, amma har yanzu matsalolin bangaren sun ki ci sun ki cinyewa.

“Dalilin a filin yake, domin kuwa wadanda suka sayar da bangaren, kansu suka sayar wa, shi ya sa yan Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin a bangaren lantarki,” a cewarsu.

(NAN)